Buhari Ya Fito a Mafarkin Wata Mata da Farin Kaya, Ta ba da Labarin me Ya Fada Mata

Buhari Ya Fito a Mafarkin Wata Mata da Farin Kaya, Ta ba da Labarin me Ya Fada Mata

  • Wata budurwa mai suna Baby Buhari ta bayyana cewa ta yi mafarkin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Ta ce ta ga marigayi Muhammadu Buhari cikin farin kaya, gashin kansa ya yi tsawo, yana murmushi cikin natsuwa
  • Mafarkin nata ya jawo ce-ce-ku-ce a dandalin sada zumunta, inda wasu ke neman fassara mafarkin da masa addu’a

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wata budurwa ‘yar Najeriya mai suna Baby Buhari ta bayyana cewa ta yi mafarki da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a ranar 13, Yuli, 2025.

Bayananta sun jawo hankalin mutane da dama a kafafen sada zumunta, inda aka rika tofa albarkacin baki kan abin da mafarkin ke iya nufi.

Muhammadu Buhari
Marigayi shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: Bashir Ahmad
Source: Facebook

Legit Hausa ta gano cewa matar ta wallafa labarin mafarkin ne a wani sako da ta fitar a shafinta na X.

Kara karanta wannan

Abin a yaba: EFCC ta kwato N42.5m da ma'aikaciyar banki ta sace wa ƴar shekara 70

Shugaba Buhari ya rasu ne a Landan lokacin da yake jinya, kuma aka yi masa jana’iza bayan dawo da gawarsa Daura, jihar Katsina.

Mafarkin Buhari ya jawo ce-ce-ku-ce

Budurwar ta ce cikin mafarkin ta, ta ga Buhari sanye da farin riga, gashin kansa ya yi tsawo, fuskarsa kuwa cikin annuri da murmushi tare da cewa:

"Nagode da addu'a,"

Matar ta ce ya gaishe ta cikin natsuwa, abin da ya sa ake fassara mafarkin a matsayin wani al’amari mai ma’ana

Wasu daga cikin masu bibiyar labarin sun yi nuni da cewa mafarkin na iya nuni da matsayin Buhari a lahira, yayin da wasu ke ganin abin tunatarwa ne ga wadanda ke kaunarsa.

Martanin ‘yan Najeriya kan mafarkin Buhari

Wani mai amfani da kafar sada zumunta mai suna Abubakar Dunoma ya fassara mafarkin yana cewa:

“Gashi mai tsawo da kyau alama ce ta mutunci da albarka. Idan mamaci ya bayyana cikin natsuwa da farin ciki, hakan na iya nuna cewa yana cikin alheri a lahira.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An lakadawa limamin masallacin Juma'a duka har ya mutu a Kwara

Ya kara da cewa idan gashin ya kasance ba da kyau ba, hakan na iya zama alamar bukatar addu’a ko sadaka a madadinsa.

“Ganin mamaci a mafarki a fahimtar Musulunci na iya zama gaskiya, domin shaidan ba zai iya daukar kamannin mamaci nagari ba,”

Inji shi

Bola Tinubu, gawar Buhari
Yadda Tinubu ya karbi gawar Buhari a Katsina. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Addu’o’i ga shugaba Buhari

Mutane da dama sun yi wa tsohon shugaban addu'a, yayin da wani mai suna Abdullahi Yakub ya rubuta cewa:

“Na ji ina sonki saboda soyayyar da muke yi wa wannan mutum mai gaskiya da kishin kasa. Muna sonka Baba, amma Allah ya fi sonka.”

Legit ta rahoto cewa AbdulRasheed Kayode Kolawole ya yi addu’a yana cewa:

“Allahu Akbar! Allah Ya faɗaɗa kabarinsa Ya kuma ba shi Aljanna Firdaus. Ina jin wata irin soyayya ta musamman gare shi tun lokacin da yake jinya, nakan yi masa addu’a kusan kullum.”

Bashir Ahmad ya kare marigayi Buhari

A wani labarin, mun kawo muku cewa Bashir Ahmad ya ba Muhammdu Buhari kariya yayin da aka fadi alakarsa da Boko Haram.

Kara karanta wannan

Musulmi, Zohra Mamdani ya lashe zaben Amurka duk da barazanar Trump

A wani taro a Abuja, tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya ce Boko Haram ta taba neman Buhari ya shiga tsakani a tattaunawa da gwamnati.

Sai dai Bashir ya ce tun a lokacin Buhari ya nisanta kansa daga bukatar tare da cewa hakan neman bata masa suna ne a siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng