Na yi mafarkin idan na yi wa yarinya karama fyade zanyi kudi - Wanda ake zargi

Na yi mafarkin idan na yi wa yarinya karama fyade zanyi kudi - Wanda ake zargi

Wani mutum mai shekaru 42 mai suna Aliyu Adamu, wanda ya yi wa karamar yarinya fyade, ya sanar da rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa cewa mafarki yayi zai yi kudi.

Kamar yadda wanda ake zargin ya sanar bayan kama shi da aka yi a garin Lafia, ya ce mafarkinsa ya nuna masa cewa zai yi kudi idan ya yi wa karamar yarinya mai shekaru 5 zuwa 10 fyade.

Wanda ake zargin ya ce: "Ni dan asalin yankin Bukan Ari ne da ke karamar hukumar Lafia. Na yi mafarkin cewa idan na yi wa yarinya mai shekaru 5 zuwa 10 fyade zan zama hamshakin mai arziki.

"A saboda hakan ne na bi mafarkina domin cikar burina."

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Bola Longe, ya kama wanda ake zargin tare da wasu mutum 44 masu laifukan da suka hada da fyade, fashi da makami da kungiyar asiri.

Ya ce an kama wanda ake zargin ne bayan ya yi wa yarinya mai shekaru 8 fyade.

Kwamishinan ya ce, an mika al'amarin gaban sashen binciken laifuka na musamman.

Hakazalika, jami'an 'yan sanda sun damke wani matashi mai shekaru 22 mai suna Zakari Mohammed a Kofar Hausa da ke karamar hukumar Keffi.

Ana zarginsa da lalata wani yaro mai shekaru 10 tare da wurga shi ta taga.

Na yi mafarkin idan na yi wa yarinya karama fyade zan kudi - Wanda ake zargi
Na yi mafarkin idan na yi wa yarinya karama fyade zan kudi - Wanda ake zargi. Hoto daga Daily Trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Harkallar diban aiki: 'Yan majalisa sun kori ministan Buhari bayan musayar yawu

Ya ce sun yi nasarar wannan kamen ne bayan rahoton da mahaifin yaron ya kaiwa 'yan sanda a hedkwatarsu da ke Keffi.

Ya ce da gaggawa 'yan sandan suka bazama neman wanda ake zargin inda daga bisani suka yi nasarar damkesa.

Kamar yadda yace: "A ranar 26 ga watan Yunin 2020, wani Abdullahi Abu da ke yankin Kurkyo na karamar hukumar Lafia ya kai wa 'yan sanda rahoto wurin karfe 12 na rana.

"Ya ce wurin karfe 11 na safe ne wani Muhammed Idris ya lalata masa dan sa mai shekaru 10 a duniya.

"Wanda ake zargin ya ja karamin yaron zuwa kango yayin da yake kokarin ba shi kudi don ya siyo masa kifi.

"Daga bisani an kama wanda ake zargin kuma ya amsa laifinsa," yace.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel