EFCC Ta Baza Komarta, Ta Nemi Taimakon FBI da Interpol don Cafke Tsohon Gwamna, Timipre Sylva
- Hukumar EFCC ta saka tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, cikin jerin mutanen da ta ke nema ruwa a jallo
- Ana zargin tsohon gwamnan Cross River da hannu a karkatar da wasu kudi da yawansu ya kai $14.8m
- Hukumar ta sanar da FBI, INTERPOL, NCA da ‘yan sanda na Birtaniya don taimaka mata wajen cafke shi domin ya dawo gida
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta fara neman tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva ruwa a jallo.
Tsohon Ministan albarkatun man fetur, Timipre Sylva, ya shiga cikin jerin mutane da EFCC take sa ido a kansu bisa zargin haɗin baki da karkatar da $14.8m.

Source: Twitter
Daily Trust ta ruwaito wata majiya daga cikin hukumar ta tabbatar da cewa EFCC ta fara neman tallafin hukumomin tsaron kasashen waje domin kama Sylva.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
EFCC na kokarin kama Sylva
Jaridar Punch ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta nemi daukin hukumomin FBI ta Amurka, INTERPOL, da hukumar NCA ta Birtaniya don kamo Timipre Sylva.
Majiyar ta shaida cewa babu inda tsohon gwamnan da ake zargi da hannu a kokarin kifar da gwamnatin Bola Tinubu zai ɓuya.
Majiyar ta ce:
“Mun tura bayanansa ga FBI, NCA da sauran hukumomin tsaro. Kusan lokaci ne kawai kafin a kawo shi Najeriya domin fuskantar shari'a”
Ana zargin Sylva da karkatar a wani ɓangare na kuɗin da Hukumar Cigaba da Sa Ido ta NCDMB ta saka a kamfanin Atlantic International Refinery and Petrochemical Limited.
An fitar da makudan kuɗin ne domin a gina matatar mai, lamarin da ake zargin karkatar da kuɗin ya jawo tsaiko.

Kara karanta wannan
Abin a yaba: EFCC ta kwato N42.5m da ma'aikaciyar banki ta sace wa ƴar shekara 70
EFCC ta tabbatar da neman Timipre Sylva
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya ce an bayar da umarnin kama Sylva ne bisa sammacin da alkali D.I. Dipeolu na Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ya bayar a ranar 6 ga Nuwamba, 2025.

Source: Facebook
A cewar Oyewale:
“Kotun ta bayar da umarni ga hukumar EFCC ko jami’an ‘yan sanda su kama wanda ake tuhuma domin gabatar da shi gaban kotu kan laifin da ake zarginsa da aikatawa.”
EFCC ta buƙaci duk wanda ke da sahihan bayanai kan inda Sylva yake da su sanar da ofishin EFCC mafi kusa ko su je wurin ‘yan sanda ko wani jami’in tsaro.
Hukumar ta lissafa ofisoshinta a Abuja, Legas, Kano, Fatakwal da Kaduna a matsayin wuraren da ake iya kai rahoto.
Hukumar EFCC na farautar Sylva
A wani labarin, kun ji cewa EFCC ta bayyana cewa tana neman Timipre Sylva bisa zargin haɗin baki da kuma karkatar da kudaden jama’a da suka kai Dala 14,859,257.
EFCC ta ce wannan adadi wani ɓangare ne na jarin da hukumar NCDMB ta saka a kamfanin Atlantic International Refinery domin gina wata matatar mai don cigaban ƙasa.
EFCC ta kuma roƙi jama’a da duk wanda ke da bayanai da suka shafi inda Sylva yake da su tuntube ta domin a taimaka wajen kamo shi domin ya fuskanci hukunci.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

