"Ina Matashi Dan Shekara 40," Obasanjo Ya Tuna Zaman da Ya Yi da Amurka a Mulkin Soja

"Ina Matashi Dan Shekara 40," Obasanjo Ya Tuna Zaman da Ya Yi da Amurka a Mulkin Soja

  • Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce lokacin mulkinsa, Amurka ba ta gaba kanta ta yi wani abu a nahiyar Afirka
  • Obasanjo ya ce duk da a lokacin da suka jagoranci Najeriya da kaki ba su wuce shekara 40, amma su na da kishin kasa da hangen nesa
  • Wannan dai na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar kawo farmaki Najeriya don kare rayukan kiristoci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ogun, Nigeria - Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya tuna yadda Amurka ke ganin Najeriya da kuma a lokacin da yake kan karagar mulkin soja.

Obasanjo ya ce lokacin da yake jagorantar Najeriya a mulkin Soja, tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter (marigayi), ba ya iya yin komai a nahiyar Afirka ba tare da ya sanar da shi ba.

Kara karanta wannan

Malaman addinin musulunci a Kano sun ba da mafita kan shirin Amurka na kawo farmaki Najeriya

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo
Hoton tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo Hoto: @Olusegun_obj
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa kalaman Obasanjo na zuwa ne yayin da ake ta ce-ce-ku-ce kan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi na kai wa Najeriya farmaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana ta martani kan barazanar Trump

Trump ya yi zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan kare dangi a Najeriya, kuma a kan haka ya ce da yiwuwar Amurka ta dauki matakin soji don yakar yan ta'adda.

Wannan baranana da shugaban Amurka ya yi ta jawo martani iri-iri daga gwamnatin Najeriya da shugabannin addini da na siyasa a fadin ƙasar nan.

Gwamnatin tarayya ta musanta zargin Trump, tana mai cewa matsalar tsaron da Najeriya ke fama da ita ta ahafi kowa, Musulmi da Kirista.

Da yake jawabi a Abeokuta, jihar Ogun, a taron matasa, Obasanjo bai ambaci sunan Trump kai tsaye ba, amma ya tuna da yadda Amurka ke mutunta Najeriya a zamanin Carter.

Obasanjo dai na da kyayyawar alaka da Shugaba Carter, wanda ya rasu a watan Disamba 2024.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

A watan Janairun bana, Obasanjo ya shirya taron tunawa da Carter a Abeokuta, inda ya yabawa tsohon shugaban Amurka wanda ya mutu yana da shekara 100.

Yadda Amurka ke neman izinin Obasanjo

A cewar Obasanjo, tun bayan samun ‘yancin kai, kasashen duniya, musamman Amurka, ta dauki Najeriya a matsayin jagorar Afirka, wanda daga baya ta rasa wannan martaba kafin gwamnatin Muritala-Obasanjo ta dawo da ita.

Ya ce lokacin da yake shugaba a mulkin Soja, Carter, wanda yake shugaban Amurka a wancan lokacin, “ba ya yin komai a Afirka ba tare da sanar da mu ba.”

“Ba wai suna neman izini ba ne, amma su na sanar da mu cewa ‘za mu yi kaza,’” in ji shi.
Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo.
Hoton tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo Hoto: Olusegun Obasanjo
Source: Getty Images

Ya kuma bayyana cewa a wancan lokacin, su na matasan sojoji ‘yan ƙasa da shekara 40, amma sun kasance masu himma da kishin ƙasa, cewar rahoton Punch.

Obasanjo ya yi magana kan Boko Haram

A wani rahoton, kun ji cewa Obasanjo ya yi gargadin cewa ta’addancin Boko Haram ya kusa zame wa yan Najeriya jiki, watau wani abu da suka saba da shi a yau da kullum.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya

Tsohon shugaban kasan ya yi kira ga jagorori su fuskanci wannan barazana cikin azama da kuma kyayyawar manufa don ganin an kawo karshen Boko Haram.

Olusegun Obasanjo ya yi tambayoyi kan yadda rikicin ya fara da kuma irin matakan da da aka dauka don ganin an kawo karshensa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262