Lokaci Ya Yi: Matar Tsohon Shugaban Najeriya, Shehu Shagari Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

Lokaci Ya Yi: Matar Tsohon Shugaban Najeriya, Shehu Shagari Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Matar marigayi tsohon shugaban kasa, Shehu Shagari, Hajiya Sutura ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da jinya a jihar Sakkwato
  • Hajiya Sutura, wacce ita kadai ta rage daga cikin matan marigayi Shehu Shagari ta rasu a yau Litinin, 10 ga watan Nuwamba, 2025
  • Iyalan Shagari sun tabbatar da wannan rashi, inda suka bayyana marigayiyar da uwa ta gari mai tawali'u, kulawa da kuma karamci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sokoto, Nigeria - Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, ta riga mu gidan gaskiya.

Rahotanni sun nuna cewa Hajiya Sutura Shehu Shagari, ita ce kadai matar tsohon shugaban kasar da ta rage a raye lafin Allah ya karbi rayuwarta a yau Litinin.

Tsohon Shugaban Kasa, Shehu Shegari.
Hoton marigayi tsohon shugaban Najeriya, Shehu Shagari Hoto: Nurudden Muhammad
Source: Facebook

Shugaban dangin Shagari, Kaftin Muhammad Bala Shagari (mai ritaya), ne ya sanar da rasuwar Hajiya Sutura a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Matar marigayi Shehu Shagari da ta rage a duniya ta rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar Shehu Shagari da ta rage ta rasu

Muhammad Bala ya ce Hajiya Sutura ta rasu da misalin karfe 3:00 na tsakar rana yau Litinin, 10 ga watan Nuwamba, 2025 tana da shekaru 89 a duniya.

A sanarwar da ya fitar, Muhammad ya ce:

“Hajiya Sutura ta rasu yau da misalin ƙarfe 3:00 na rana, tana da shekara 79, bayan ta yi fama da doguwar jinya.”

Kyaftin Shagari ya bayyana marigayiyar a matsayin abin koyi wajen tawali’u, natsuwa da karamci, wacce ta kasance uwar gida mai cike da kulawa.

Ya kuma bayyana Hajiya Sutura da uwa kuma kaka ta gari mai yi wa kowa fatan alheri, wacce rayuwarta ta kasance cike da mutunci da tausayi.

Hadimin Gwamna Aliyu ya yi ta'aziyya

Gwamnatin Sakkwato ta hannun mai babban mai taimaka wa Gwamna Ahmed Aliyu kan harkokin dabarun sadarwa, Nuruddeen Muhammad Mahe ta tabbatar da rasuwar.

A wata sanarwa da hadimin gwamnan ya wallafa a shafin Facebook, ya ce Hajiya Sutura ta rasu ne a asibitin Saraki da ke cikin birin Sakkwato.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

Sanarwar ta ce:

"Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mun sami labarin rasuwar Hajiya Sutura Shehu Shagari, matar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, wacce ita ce kadai daga cikin matansa da ta rage da rai.
Hajiya Sutura ta rasu a Asibitin Saraki da ke Sakkwato, bayan ta yi fama da doguwar jinya. Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta mata kura-kuranta, Ya jikanta, Ya kuma ba ta Aljannatul Firdaus. Ameen.
"Za a sanar da lokacin jana’izarta a nan gaba, in sha Allah."
Taswirar jihar Sakkwato.
Hoton taswirar jihar Sakkwato Hoto: Legit.ng
Source: Original

Malamin Izala a Funtua ya kwanta dama

A wani labarin, kun ji cewa babban limamin masallacim Juma'a na yan Izala da ke garin Funtua a jihar Katsina, Sheikh Goni Imam Sa'idu Musa ya riga mu gidan gaskiya.

Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawa, Muntaru Dandutse ya tabbatar da rasuwar malamin a sanarwar da ya fitar ranar Litinin.

Ɗandutse ya ce rasuwar malamin babban rashi ne ga mutanen Funtua, Jihar Katsina, da kuma al'ummar musulmi baki daya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262