Tirkashi: EFCC Ta Kafe Hoton Timipre Sylva, Ana Neman Tsohon Gwamna Ruwa a Jallo
- EFCC ta ayyana Timipre Sylva, tsohon gwamnan jihar Bayelsa, a matsayin wanda ake nema bisa zargin karkatar da $14.8m
- Hukumar ta ce kudin na cikin jarin da hukumar NCDMB ta saka don gina matatar man fetur a kamfanin Atlantic Refinery
- Kotu ta bayar da sammacin kama shi tun daga ranar 6 ga Nuwamba, 2025 bayan majalisa ta fara binciken badakalar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ayyana tsohon karamin ministan man fetur, Timipre Sylva a matsayin wanda take nema ruwa a jallo.
EFCC ta baza komar kama Timipre Sylva, wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar Bayelsa, ne bisa zargin karkatar da kudaden gwamnati.

Source: Twitter
Zargin da ake yi wa tsohon gwamnan Bayelsa

Kara karanta wannan
Abin a yaba: EFCC ta kwato N42.5m da ma'aikaciyar banki ta sace wa ƴar shekara 70
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Dele Oyewale, ya fitar ranar Litinin a Abuja, kuma aka wallafa a shafin EFCC na X.
A cewar EFCC, Sylva ya karkatar da adadin kudin da suka kai dalar Amurka 14,859,257, wani ɓangare na jarin hukumar NCDMB.
Sanarwar ta bayyana cewa hukumar NCDMB ta saka kudin ne a matsayin jari a matatar man fetur ta Atlantic International, domin gina wata matatar mai a Najeriya.
EFCC na farautar tsohon gwamna, Sylva
A cikin sanarwar, EFCC ta ce:
“Ana sanar da jama’a cewa, ana neman Timipre Sylva, tsohon karamin ministan man fetur kuma tsohon gwamnan jihar Bayelsa, wanda hotonsa ke sama ruwa a jallo.
"Ana nemansa ne bisa zargin haɗin baki da karkatar da kudin da suka kai dala 14,859,257, wani ɓangare na jarin da hukumar NCDMB ta saka a kamfanin Atlantic International domin gina matatar mai.”
Hukumar ta ƙara da cewa:
“Sylva, mai shekara 61, dan asalin karamar hukumar Brass ta jihar Bayelsa ne. Wannan sanarwar ta fito ne bisa sammacin kamu da kotun jiha ta Legas ta bayar a ranar 6 ga Nuwamba, 2025.”

Source: Facebook
Kama gwamna: EFCC ta neman agajin jama'a
Hukumar EFCC ta kuma roki 'yan Najeriya da su taimaka mata a kokarin da take yi na kama tsohon gwamnan na Bayelsa.
Sanarwar ta ce:
“Duk wanda ke da sahihin bayani game da inda yake, ya tuntubi hukumar a ofisoshinta dake Ibadan, Uyo, Sokoto, Maiduguri, Benin, Makurdi, Kaduna, Ilorin, Enugu, Kano, Lagos, Gombe, Port Harcourt ko Abuja."
Hukumar ta kuma bayyana cewa ana iya tuntuɓarta ta layin waya 08093322644, ko ta adireshin imel ɗinta info@efcc.gov.ng, ko kuma a kai rahoto ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko sauran hukumomin tsaro.
Ana zargin hannun Sylva a yunkurin juyin mulki
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an DIA tare da hadin gwiwar hukumar NFIU da EFCC sun gano kudin da aka so amfani da su wajen yunkurin kifar da gwamnatin Bola Tinubu.
Rahotanni sun nuna cewa binciken ya kai ga asusun tsohon gwamnan Jihar Bayelsa kuma tsohon karamin Ministan man fetur, Cif Timipre Sylva.
Wasu majiyoyi sun bayyana cewa wasu jami’an soja da aka kama da hannu a shirin juyin mulkin ne suka tona asirin Timpre Sylva, wanda ya ki dawowa Najeriya daga kasar waje.
Asali: Legit.ng

