Arewa ko Kudu: Sanata Nwoko Ya Fadi Jihar da Tinubu Ke Goyon Bayan Kirkirowa
- Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa ya yi karin haske kan yunkurin kirkiro sabuwar jiha a Najeriya
- Ned Nwoko ya bayyana cewa jiha daya kawai za a kara kirkirowa a Najeriya kuma wannan jihar ita ce Anioma
- Sanatan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya shirya rattaba hannu kan kudirin kafa jihar da zarar an kammala bin duk matakan da suka dace
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa, ya bayyana cewa an samu gagarumar nasara a yunkurin kafa jihar Anioma.
Sanata Ned Nwoko ya ce an samu nasarar ne bayan samun goyon bayan kwamitocin gyaran kundin tsarin mulki da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta ce Nwoko ya yi wannan bayani ne a wurin taron kungiyar Izu Anioma Towns Union da aka gudanar a Abuja a karshen mako.

Kara karanta wannan
Anioma: Shugaba Tinubu, Akpabio da sanatoci 97 sun goyi bayan kirkiro jiha 1 a Najeriya
A wurin taron, an kaddamar da bikin al’adar Anioma karo na farko.
Tinubu da sanatoci na goyon bayan Anioma
Ya ce sanatoci 97 sun riga sun sanya hannu kan takardar da ke goyon bayan kirkirar sabuwar jihar, yana mai bayyana wannan goyon baya a matsayin abin da bai taɓa faruwa ba a tarihin siyasar Najeriya.
Sanatan ya bayyana cewa kudirin da ya gabatar yana neman a samar da jihar Anioma daga cikin kananan hukumomi tara na Delta ta Arewa, ciki har da hudu daga Aniocha da Oshimili, biyu daga Ika, da uku daga Ndokwa.
Ya kara da cewa wasu al’ummomi makwabta, ciki har da Igbanke, sun nuna sha’awar shiga cikin sabuwar jihar da ake shirin kafawa.
“Jiha guda ɗaya kawai za a kirkira a Najeriya, kuma wannan jiha ita ce Anioma."
- Sanata Ned Nwoko
Nwoko ya bayyana cewa kwamitocin majalisar dattawa da ta wakilai kan gyaran kundin tsarin mulki, waɗanda ke da wakilci daga dukkan jihohin kasar nan, sun amince cewa dole ne yankin Kudu maso Gabas ya samu jiha ta shida don daidaita tsarin yankuna.

Kara karanta wannan
Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla
Ya ce wannan shiri ya samu cikakken goyon bayan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, kuma Shugaba Tinubu ya nuna shirinsa na amincewa da kirkirar jihar bayan kammala dukkan matakan kundin tsarin mulki.
“Mun yi aikinmu yadda ya kamata. Mun yi kamun kafa na siyasa, tattaunawa, da shawarwari da ake ci gaba da yi. Ba mu bar komai a baya ba."
- Sanata Ned Nwoko

Source: Instagram
Za a zauna kan jihar Anioma
Sanatan ya kara da cewa shugabanni daga yankin Kudu maso Gabas, sarakunan gargajiya, da wakilan Anioma za su gana a Awka, jihar Anambra, a karshen mako mai zuwa don amincewa da Anioma a matsayin sabuwar jihar da za a kirkira a yankin.
Ya ce bayan kammala dukkanin matakan da ya kamata a bi, Shugaba Tinubu zai sanya hannu kan takardar kafa sabuwar jihar a wani biki na tarihi.
Nwoko ya kuma roki al’ummar Anioma da su ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinki ɗaya, yana mai cewa nasara ta kusa zuwa.
“Ba ni na fara wannan gwagwarmaya ba, amma zan gama ta. Jihar Anioma za ta zama sabon tarihi."
- Sanata Ned Nwoko
Tinubu ya taya Soludo murna
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da sakon taya murna ga gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo.
Shugaba Tinubu ya taya Gwamna Soludo murna ne kan nasarar da ya samu a zaben gwamnan da aka gudanar a jihar Anambra.
Tinubu ya bayyana cewa nasarar da gwamnan ya samu ta nuna cewa mutanen jihar sun gamsu da salon shugabancinsa.
Asali: Legit.ng
