Kwana Ya Kare: Babban Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Goni Imam Sa'id Ya Rasu
- Malamin addinin musulunci kuma limamin masallacim Izala na garin Funtua da ke jihar Katsina, Sheikh Goni Imam Sa'id ya kwanta dama
- Sanatan Funtua (Katsina ta Kudu), Muntari Dandutse ya yi alhinin rasuwar shehin malamin a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin
- Dantsute ya bayyana Sheikh Goni a matsayin mutumin kirki, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimta wa addinin musulunci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Funtua, jihar Katsina - Babban malamin addinin musulunci a garin Funtua da ke jihar Katsina, Sheikh Goni Imam Sa'id Musa ya riga mu gidan gaskiya.
Marigayi malamin, wanda shi ne babban limamin masallacin 'yan izala da ke garin Funtua (JIBWIS) ya rasu ne ranar Lahadi da daddare bayan fama da jinya.

Source: Facebook
Malamin Izala a Funtua ya rasu
Sanata mai wakiltar Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawa, Muntaru Dandutse ya tabbatar da rasuwar malamin a wata sanarwa da ya wallafa a Facebook yau Litinin da safe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rahotanni daga yankin sun nuna cewa za a yi jana'izarsa da misalin karfe 2:00 na rana yau Litinin a filin makarantar firamare ta Aya da ke cikin garin Funtua.
Sanata Muntari Dandutse bayyana jimaminsa kan rasuwar Sheikh Goni Imam Sa’idu Musa Funtua, tare da mika sakon ta'aziyya.
Musulmin Najeriya sun yi rashi
Ɗandutse ya ce rasuwar malamin babban rashi ne ga mutanen Funtua, Jihar Katsina, da kuma al'ummar musulmi baki daya.
Sanatan Funtua ya ce:
"Sheikh Goni Sa’idu Musa Funtua ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addinin Musulunci, yana koyar da Al-Qur’ani mai girma, fadakarwa da gina al'umma mai ilimi, zaman lafiya da kyawawan dabi’u.
Dandutse ya mika sakon ta'aziyya
Sanatan ya ƙara da roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa, Ya jikansa da rahama, Ya sa Aljanna ta zama makomarsa.
"Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya jikansa da rahama. Ya ba iyalansa, ɗalibansa da al’umma haƙuri da juriya wajen jure wannan babban rashi," in ji shi.

Source: Facebook
Ɗandutse ya ce rayuwar Sheikh Goni Liman Sa’idu Musa ta zama abin alfahari ga yankin Funtua da Jihar Katsina baki ɗaya saboda irin ayyukan alheri da ya bari a bayansa.
"Haka rayuwa take, kowa zai tafi, amma kyawawan ayyuka su ne gado na gaskiya. Sheikh Goni Liman Sa’idu Musa ya bar tarihi mai daraja,” in ji shi.
A ƙarshe, Sanata Ɗandutse ya roƙi Allah Ya jikansa, Ya sa kabarinsa ya zama lambun Aljanna, kuma Ya ba wa al’umma ikon bin sahunsa cikin kyawawan ayyuka.
Malamin musulunci a Kano ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa na'ibin babban limamin masallacin Jumma'a na Al-Furqan Kano, Malam Aminu Adam Dorayi ya riga mu gidan gaskiya.
Limamin masallacim Al-Furqan, Sheikh Bashir Aliyu Umar ya tabbatar da rasuwar Malam Aliyu Adam, tare da addu'ar Allah Ya jikansa.
utane da dama musamman jama'ar Kano sun tura sakon ta'aziyya da addu'ar Allah Ya jikan Malam Aminu Adam kuma ya gafarta masa kura-kuransa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

