An Rage Kudin Hajjin 2026 a Najeriya, NAHCON Ta Fitar da Adadin da za a Biya
- An fitar da kudin aikin Hajjin 2026 bayan shugaba Bola Tinubu ya umurci hukumar NAHCON da ta sake duba kudin
- Sabon jadawalin biyan kudi ya bai wa maniyyata wa’adi har zuwa ranar 5 ga Disamba, 2025 don kammala biyan su
- An rage kudin zuwa tsakanin N7.5m da N7.9m bisa ga yankuna, wanda ya nuna sauki idan aka kwatanta da shekarar 2025
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta amince da sabon tsarin kudin aikin Hajji na shekarar 2026 bayan sake nazari da aka yi.
Wannan na zuwa ne bayan umarnin shugaban kasa da ya bayar ranar 6, Oktoba, 2025 domin rage nauyin da maniyyata ke dauka wajen biyan kudin tafiya zuwa kasa mai tsarki.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan rage kudin ne a wani sako da hukumar NAHCON ta wallafa a shafinta na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sabon tsarin kudin aikin Hajji a Najeriya
Sabon kudin aikin Hajji na 2026 da hukumar NAHCON ta fitar ya nuna cewa an rage farashin idan aka kwatanta da na shekarar 2025.
A cewar hukumar:
- Masu zuwa daga yankin Borno da Adamawa za su biya ₦7,579,020.96
- Masu zuwa daga sauran yankunan Arewa za su biya ₦7,696,769.76
- Masu zuwa daga yankunan Kudu za su biya ₦7,991,141.76
A shekarar 2025 kuwa, kudin aikin Hajji ya kasance tsakanin ₦8,327,125.59 zuwa ₦8,784,085.59, wanda ke nuna cewa an samu ragin tsakanin ₦748,000 zuwa ₦792,000 a kowanne yanki.
NAHCON ta ce wannan sauki ya biyo bayan kokarin gwamnati na rage nauyin tafiya Hajji domin bai wa ‘yan kasa damar gudanar da ibada cikin sauki da kwanciyar hankali.
Gwamnati ta dage wa’adin biyan kudi
Hukumar ta kuma sanar da cewa sabon wa’adin karshe na biyan kudin aikin Hajji shi ne 5, Disamba, 2025, domin bai wa maniyyata karin lokaci su kammala biyan kudin su.

Source: Facebook
A cewar hukumar, wannan mataki zai ba da damar tattara kudin a kan lokaci tare da mika su ga Babban Bankin Najeriya (CBN), domin tabbatar da shirye-shirye kafin tafiyar maniyyata.
Umarnin rage kudin Hajji da aka yi
Daily Trust ta rahoto cewa a Okotoban 2025 mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce shugaba Bola Tinubu ya bukaci a rage kudin aikin Hajji.
A lokacin, ya bukaci hukumomin jihohi da masu ruwa da tsaki da su yi aiki kafada da kafada da NAHCON domin tabbatar da cewa an yi aikin ba tare da tangarda ba.
Shettima ya kuma gargadi jami’an gwamnati da su guji jinkirta biyan kudin domin kada hakan ya kawo cikas ga shirin tafiyar Hajji na 2026.
An rage wa Najeriya kujerun Hajji
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sanar da cewa Saudiyya ta rage mata adadin kujerun Hajji a bana.
Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, ta bayyana cewa a 2026, kasar Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 66,910 ne kacal.
NAHCOn ta ce rage kudin ya biyo bayan rashin cike guraben kujerun da ake ba Najeriya ne a shekaru da suka wuce.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


