‘Ba fa Maganar Kishin Kiristoci ba ne’: Gwamna Sule Ya Gano Makircin Trump
- Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa shi ma ya yi magana kan barazanar da Shugaba Donald Trump ya yi ga Najeriya
- Gwamnan ya ce batun kisan gilla da Amurka ke danganta da Kiristoci a Najeriya karya ne, don Amurka tana kare muradunta ne kawai
- Sule ya gargadi ’yan siyasa da su daina tayar da rikicin addini don neman kuri’u, yana mai cewa gwamnatinsa ta Nasarawa ta kowa da kowa ne
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lafia, Nasarawa - Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, ya musanta ikirarin cewa akwai kisan gilla kan Kiristoci a Najeriya.
Gwamna ya ce ba wai zargin kisan Kiristoci ba ne yasa Amurka ke shirin kai farmaki Najeriya, akwai dai wata manufa.

Source: Facebook
Gwamna Sule ya fadi damuwar Amurka
Gwamnan ya bayyana haka ne a wajen taron kide-kiden Kiristoci na kasa karo na 30 a Lafia, jihar Nasarawa, cewar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, Amurka ba ta damu da wani addini ko ƙasa ba, illa kawai abin da zai amfani ƙasarta.
Injiniya Sule ya ce ya san halayyar Amurka sosai, domin ya yi karatu, aiki, da zama a can shekaru da dama, inda ya gano cewa kasar tana kare muradunta ne kawai.
“Ina da ilimin yadda Amurka take aiki. Na zauna a can, na yi aiki, kuma na ga yadda suke kare muradunsu. Idan dai an taba muradin Amurka, to tabbas za ta mayar da martani.”
- Abdullahi Sule
Ya kara da cewa, Shugaba Bola Tinubu ma ya fahimci wannan tun da ya taba zama a Amurka, don haka ya dauki diflomasiyya a matsayin hanya mafi dacewa wajen magance lamarin.

Source: Getty Images
Gwamna ya bada misali da rikicin Rasha, Ukraine
Gwamnan ya yi nuni da yadda rikicin Rasha da Ukraine ya janyo mutuwa da asarar dukiya, yana mai cewa yakin da Amurka ke barazanar kawo wa Najeriya zai fi haka barna.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Kasar Rasha ta tsoma baki kan shirin Amurka na kai farmaki Najeriya
Sule ya kuma zargi wasu ‘yan siyasa da tayar da fitinar addini don cimma muradunsu na siyasa, ya ce irin wadannan mutane ne ke haddasa rabuwar kawuna tsakanin Musulmi da Kirista.
“Idan zabe ya zo, sai a fara maganar addini. Amma idan suna rabon kudi ko mukamai, babu wanda ke tuna da addini. Kada ku bari su rude ku.”
- Abdullahi Sule
Ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar zama ta kowa da kowa a Nasarawa, ba tare da nuna bambanci ba, kuma wannan ne sirrin zaman lafiya a jihar.
Gwamna Sule ya godewa kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) bisa zaben Nasarawa a matsayin wurin taro, yana mai cewa hakan ya tabbatar da cewa jihar tana maraba da kowa.
An musanta shigowar sojojin Amurka a Najeriya
An ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi magana bayan yada wani bidiyo a kafofin sadarwa da aka ce sojojin Amurka sun fara sauka a Najeriya.
An yada wani faifan bidiyo da ya bazu a intanet da ke cewa sojojin Amurka sun isa Jihar Rivers domin kaddamar da umarnin Donald Trump.

Kara karanta wannan
'Abin da zan faɗawa Trump ido da ido, idan na haɗu da shi': Barau Jibrin ya fusata
Mai taimaka wa Shugaba Tinubu kan kafofin sada zumunta, Dada Olusegun, ya bayyana cewa labarin karya ne don ya hana yada jita-jita.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
