Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla

Kungiyar Musulman Najeriya ta yi tsokaci kan ikrarin Trump na yiwa Kirisoci kisan gilla

  • Kungiyar Musulmai ta NSCIA ta ce sam babu wani lamari mai kama da kisan Kiristoci zalla a Najeriya
  • Kungiyar ta ce wannan ba komai bane face kitsa wata mummunar manufa ta siyasar duniya kan Najeriya
  • Ya bayyana abubuwan da ya kamata Trump ya yi a madadin zafafa kamalai da manufa kan kasar mai mutane sama da miliyan 200

FCT, Abuja - Hukumar gamayyar harkokin addinin Musulunci ta NSCIA a Najeriya ta musanta ikirarin da ake yadawa na cewa ana kisan Kiristoci a Najeriya, tana mai cewa ikirarin karya ne, mai hadari, kuma shiryayye.

A yayin taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, Sakataren Janar na Hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana cewa ikirarin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa karya ne zunzurutu.

Ya kuma bayyana cewa, hakan wata manufa ce ta siyasa da ake yadawa don ganin an gwara kan mabiya addinan Islama da Kirista fada a kasar.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

Musulmai sun ce ba a kashe Kirista a Najeriya
An karyata ikrarin Trump kan kisan Kiristoci a Najeriya | Hotuna: SAUL LOEB/AFP(hoton Trump), Emmanuel Osodi/Anadolu. An yi amfani da hotunan nan ne don misali, ba na ainihin abin da ya faru bane
Source: Getty Images

Manyan matsalolin Najeriya a yanzu

Ya bayyana cewa tashin hankali da ake samu a wasu sassan kasar ya samo asali ne daga talauci da hijirar da sauyin yanayi ya janyo, ba azabtarwa da tsangwama ta addini ba, rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa:

“Ina tabbatar da cewa a Najeriya babu ta’addanci kan Kiristoci. Babu ta’addanci kan Musulmi. Babu rashin jituwa tsakanin addinai a Najeriya. Matsalar Najeriya ita ce ta talauci, sauyin yanayi, mulkin Rashin adalci a baya-bayan nan, da kuma ‘yan ta’adda da ke kashe mutane ba tare da bambanci ba, yayin da wasu kasashen duniya ke son cin gajiyar wannan hali don cimma manufar siyasa.”

Maganar NSCIA ya biyo bayan sabuwar muhawara da aka fara sakamakon maganganun da Shugaba Donald Trump na Amurka ya yi kwanan nan, inda ya yi Allah-wadai da kisan taron Kiristoci a Najeriya.

Trump zai kawo yaki Najeriya

Hakazalika, ya umurci Ma’aikatar Yaki ta Amurka “ta shirya don yiwuwar daukar mataki,” yana mai cewa harin da sojojin Amurka za su kai zai kasance “da sauri, mai tsanani, kuma mai kyau,” idan gwamnatin Najeriya ta bar kisan ya ci gaba.

Kara karanta wannan

A karon farko, Tinubu ya fadi abin da Najeriya ke yi kan barazanar Trump

Sakataren NSCIA ya zargi wasu kungiyoyin ‘yan Najeriya ‘yan aware, masu yiwa kasashen waje aiki, da ‘yan siyasan Amurka da amfani da rashin tsaro a Najeriya don amfanar kansu ko siyasarsu

Ya kara da cewa:

“Wadannan kungiyoyi na yada kididdiga da bidiyo da aka kirkira don rinjayar da gwamnatocin kasashen yamma, musamman Amurka, su dauki matakai masu tsanani kan Najeriya.”

Kira ga gwamnatin Najeriya da ma duniya

Har ila yau, ya ce sabuwar matsayar Amurka ta sanya Najeriya a matsayin “ƙasa mai abin damuwa na musamman” wata dabara ce ta siyasa, ba wai gaskiyar abin da ke faruwa a kasar ba.

NSCIA ta bukaci gwamnatin Najeriya da al’ummar duniya su karyata wannan “rikici da aka kirkira,” tare da rokon Shugaba Donald Trump da ya taya Najeriya wurin yaki da irin wannan ta hanyar tallafin kayan aiki maimakon yada labaran karya.

Oloyede ya jaddada cewa Musulmai da Kiristoci dole su tsaya tsayin daka wajen yaki da ta’addanci da manyan laifuffuka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng