Bidiyo: Rigima Ta Barke Tsakanin Mataimakin Gwamna da Sojan Najeriya a Wajen Zabe
- An samu 'yar hatsaniya tsakanin mataimakin gwamnan Anambra, Dr Onyekachukwu Ibezim da wasu jami'an sojojin Najeriya
- Bidiyo ya nuna lokacin da mataimakin gwamnan ke titsiye wani jami'in soja saboda ya gansa a wurin tattara sakamakon zabe
- Masana harkar doka sun bayyana cewa sojojin sun yi aiki bisa ka’ida domin sun je ne kare rayukan ‘yan NYSC da jami’an zaɓe
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Anambra - An samu sababbin bayanai game da bidiyon da ya yadu a kafafen sada zumunta inda aka ana cacar baki tsakanin mataimakin gwamnan Anambra da wasu sojoji.
An ce mataimakin gwamnan, Dr Onyekachukwu Ibezim ya kalubalanci wani soja a lokacin zaɓen gwamna da aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

Source: Twitter
Mataimakin gwamnan Anambra ya zazzage sojoji
Bidiyon da Zagazola Makama ya dora a shafinsa na X ya nuna Dr. Ibezim yana daga murya yana tambayar dalilin da ya sa sojoji suka je wurin tattara sakamakon zaɓe a ofishin INEC da ke Awka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar majiyoyi daga rundunar sojin Najeriya, sojojin sun je wurin ne bayan kiran gaggawa daga Ko’odinatar NYSC ta jihar Anambra, Mrs. Pauline Ojisua.
Majiyoyin sun bayyana cewa da misalin karfe 8:20 na safe, Mrs. Ojisua ta tuntubi rundunar sojoji ta 302 Artillery Regiment (G.S) tana neman agajin gaggawa saboda ‘yan daba sun rufe jami’an INEC da ‘yan NYSC a Unguwar Ukwu Oji Umubele, Awka Ward 5, cikin karamar hukumar Awka South, bayan jami’in tattara sakamakon zabe ya tsere.
“Sojoji sun isa wurin cikin gaggawa, suka ceci jami’an, sannan suka raka su cikin aminci zuwa ofishin INEC inda aka ci gaba da tattara sakamakon ba tare da wani tashin hankali ba,” in ji majiyar tsaro.
Sai dai, bayan zuwan su ne, mataimakin gwamna da wasu daga cikin abokan siyasarsa suka hana su shiga, suna kalubalantar zuwansu wurin tattara sakamakon.
Soja ya fadi dalilin zuwansu wajen tattara kuri'u
Bidiyon da ya yadu ya nuna mataimakin gwamnan yana ta tsawatarwa sojan, yana mai cewa sojoji ba su da hurumin shiga cibiyar tattara sakamako, duk da cewa an sanar da shi cewa jami’an gwamnati ne suka nemi agajinsu.
An kuma ga sojan ya nutsu ya na jin maganganun mataimakin gwamnan, inda daga bisani ya yi kokarin yi masa bayani na kira gaggawa da aka yi masu.
“Madam, me kika fada mun lokacin da kika kira ni?” Sojan ya tambayi jami’ar INEC kafin bidiyon ya yanke.
Wata majiyar tsaro ta ce ta iya yiwu wa mataimakin gwamnan ya fusata ne kawai saboda sojojin sun hana ‘yan dabar siyasa mamaye cibiyar tattara sakamakon zaben.

Source: Original
Masana sun magantu kan wannan bidiyo
Masani a harkar doka, Kelvin Martings, ya bayyana cewa sojoji sun gudanar da aiki bisa doka, kuma sun yi abin da ya dace, domin jami’ar NYSC — wacce ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya — ita ce ta nemi kariya daga gare su.
Ya kuma yi Allah wadai da irin yadda mataimakin gwamnan ya rufe sojojin da masifa, yana mai cewa:
“Hana jami’an tsaro yin aikin su a lokacin da aka yi masu kiran gaggawa abu ne da bai kamata ba.”
Wasu majiyoyi ma sun tabbatar cewa da ba don sojoji sun isa wurin cikin lokaci ba, da jami’an NYSC da INEC sun shiga haɗari.
INEC dai ba ta fitar da sanarwa kan lamarin ba har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.
Jami'ar INEC ta suma a zaben Anambra
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata jami’ar INEC ta yanke jiki ta sume a yayin zaben gwamnan Anambra saboda hayaniya da matsalar na’urar BVAS.
An samu rahoto cewa dubban masu jefa kuri’a a Enugwu-Ukwu sun kasa kada kuri’unsu saboda BVAS ta gaza tantance katin masu zabe.
An ce jami’ar, Miss Blessing Egoigwe, ta sume ne yayin da jama’a suka fara hayaniya saboda gazawar na’urar BVAS wajen tantance katin masu zabe da kuma yatsun hannunsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


