Zaben Anambra: Abin da Soludo Ya Ce bayan Samun Wa'adi na 2
- Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya yi tsokaci kan nasarar da ya sake samu a zabe
- Farfesa Soludo ya yabawa mutanen jihar Anambra kan yadda suka sake ba shi damar mulkarsu har na tsawon shekara hudu masu zuwa
- Gwamnan ya bayyana cewa mutanen jihar ba su ga komai ba domin zai ci gaba da gudanar da ayyuka masu muhimmanci
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Gwamna Chukwuma Soludo ya yi magana bayan nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar a jihar Anambra.
Gwamna Soludo ya gode wa jama’ar jihar Anambra kan sake zabensa, yana mai cewa wannan amincewa sabon tarihi ne da nasara ga jihar.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce Gwamna Soludo ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi bayan hukumar zaɓe ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Soludo ya sake samun wa’adi na biyu tare da mataimakinsa, Dr. Onyeka Ibezim.
Me Gwamna Soludo ya ce kan nasararsa?
A yayin da yake jawabi ga magoya bayansa, Soludo ya ce jama’ar jihar sun aika da sako mai karfi na gamsuwa da amincewa da gwamnatinsa.
Ya tuna cewa a 2021, nasararsa ta farko ta zo ne a lokacin da fitowar masu kaɗa kuri’a ta yi kasa, amma ya lura cewa wannan zaɓen na baya-bayan nan, mutane sun fito sosai.
“Shekaru huɗu da suka wuce, kun yi magana kuma kuka ba mu amanar ku. A lokacin ne Anambra ta fara gwajin BVAS karo na farko, kuma fitowar jama’a ta yi kasa sosai. Kun zaɓe mu da kuri’u 112,000."
"A wannan karon, kun yi magana da karfi. Bisa kaso na masu rajista da suka fito, kusan kashi 22 cikin 100 ne suka kada kuri’a a wannan zaɓe, abin da bai taɓa faruwa ba a baya. Kun karya tarihin kashi 20 cikin 100.”
- Gwamna Chukwuma Soludo
Gwamna Soludo ya kuma bayyana cewa nasarar da ya samu ta kafa sabon tarihin siyasa a Anambra, inda ya nuna cewa tun daga 1999, gwamnoni uku kacal aka sake zaɓa a wa’adi na biyu.
Ya ce goyon bayan da ya samu a wannan zaɓen shi ne mafi rinjaye cikin tarihin jihar.
“A 2010, wani gwamna ya samu nasarar wa’adi na biyu da kashi 31 cikin 100 na kuri’un da aka kada. A 2017, wani ya samu da kashi 56 cikin 100."
"Amma a wannan zaɓen, kun sake zaɓen mu da kashi 73 cikin 100 na kuri’un da aka kada. Wannan babban abu ne da ya cika ni da tawali’u da godiya."
- Gwamna Chukwuma Soludo
Soludo ya yi albishir ga mutanen Anambra
Ya tabbatar wa jama’ar jihar cewa gwamnatinsa za ta kara kaimi wajen kawo ci gaba a duk faɗin Anambra.

Source: Twitter
“Mun nemi wannan aiki, kuma kun ba mu shi shekaru huɗu da suka gabata. Abin da zan iya cewa, kamar yadda muka faɗa a lokacin kamfe, shi ne, ba ku ga komai ba tukuna."
"Kamar yadda Amurkawa ke faɗa, ‘ba a yi komai ba tukuna’ da wannan amincewa da haɗin kai tsakanina da ku, zan iya cewa cikin shekaru huɗu masu zuwa, Anambra za ta shaida cigaba fiye da duk abin da aka gani a baya.”
- Gwamna Chukwuma Soludo
Soludo ya cika baki kan zaben Anambra
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya hango nasara a zaben gwamnan jihar.
Gwamna Soludo ya bayyana cewa jam'iyyarsa ta APGA za ta samu gagarumar nasarar a zaben gwamnan jihar na ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.
Hakazalika ya nuna cewa 'yan adawa ba za su kai labari ba a zaben domin an riga da an fi karfinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


