Bidiyo: An ga 'Yan Sanda Suna Harba Bindiga bayan Soludo Ya Lashe Zaben Anambra

Bidiyo: An ga 'Yan Sanda Suna Harba Bindiga bayan Soludo Ya Lashe Zaben Anambra

  • Jami’an ‘yan sanda da ke gadin Gwamna Charles Soludo sun yi harbe-harbe bayan nasararsa a zaɓen gwamnan Anambra
  • Soludo na APGA ya lashe zabe a kananan hukumomi 21, inda ya samu kuri’u 422,664 tare da doke Nicholas Ukachukwu na APC
  • Har zuwa lokacin wallafa wannan rahoto, ‘yan sanda ba su ce uffan ba kan dalilin harbe-harben da jami'ansu suka yi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - An samu ɗan tashin hankali a Isuofia, karamar hukumar Aguata, bayan jami’an ‘yan sanda da ke gadin Gwamna Charles Soludo sun yi harbe-harbe a saman iska.

domin murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan Anambra da aka gudanar a ranar Asabar, 8 ga Nuwamba, 2025.

An ga bidiyon 'yan sanda suna harbe-harben bindiga bayan nasarar zaben Soludo a Anambra.
Hoto daga bidiyon da ya nuna 'yan sanda suna harbe-harbe bayan Soludo ya lashe zaben Anambra. Hoto: Channels TV.
Source: UGC

'Yansanda sun yi harbi a gidan Soludo

Rahotanni sun nuna cewa jami’an sun fara murnar ne bayan hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana Soludo na jam’iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen, in ji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Anambra: Bayan kai ruwa rana, INEC ta sanar da wanda ya lashe zaben gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta ya nuna jami’an tsaro suna murna da harbi a sama a cikin gidan Soludo, yayin da magoya bayansa ke rera wakoki da rawar murna.

Wannan dai bakon abu ne ga mafi yawan mutane, don ba a saba ganin jami'an tsaro suna harba bindiga don murnar wani d'an siyasa ya ci zabe ba.

Rahoton The Whistler ya nuna cewa, doka ba ta sahalewa 'yan sanda amfani da makami a yayin zabe ba tare da wani kwakkwaran dalili ba, wannan kuwa ya hada har da harbi a saman iska.

Yayin da ake sa ran 'yan sanda za su rike aikinsu da kwarewa, ana iya tuhumar su da aikata laifi daga yadda suka yi amfani da makamansu, kuma kotu ce za ta iya yanke hukunci kan ko ya dace su yi harbin ko a'a.

Sakamakon zaɓen gwamnan anambra 2025

A cewar hukumar INEC, Soludo ya samu kuri’u 422,664, wanda ya ba shi damar doke Nicholas Ukachukwu na jam'iyyasr APC wanda ya samu kuri’u 99,445.

Kara karanta wannan

Sakamakon zaben Anambra: Yadda APGA ta samu kuri'u 422664 a kananan hukumomi 21

A hannu daya, Paul Chukwuma na jam'iyyar YPP ya zo na uku da kuri’u 37,753, yayin da John Nwosu na ADC ya samu 8,208.

George Moghalu na Labour Party (LP) ya samu kuri'u 10,576, sannan Jude Ezenwafor na jam'iyyar PDP ya samu 1,401 kacal.

Soludo ya lashe dukkannin kananan hukumomi 21 na jihar, abin da ya tabbatar da tazarcensa da tazara mai rinjaye, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Rundunar 'yan sanda ba ta ce uffan ba game da harbe-harben bindiga da jami'ansu suka yi a Anambra.
Babban sufetan 'yan sanda na kasa, IGP Kayode Agbetokun yana aiki a ofishinsa da ke Abuja. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Rundunar ‘yan sanda ta yi shiru

Duk da cewar bidiyon harbe-harben ya karade yanar gizo, rundunar ‘yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa ba game da abin da ya faru ba.

Wasu mazauna garin sun ce sun firgita, inda suka rika tunanin ko 'yan bindiga ne suka kawo masu hari, kafin daga baya su gane cewa murnar nasara ce kawai.

Rahotanni sun tabbatar da cewa babu wanda ya ji rauni, yayin da jami’an tsaro daga baya suka kwantar da hankalin jama'a a unguwar.

Kalli bidiyon a nan kasa:

EFCC sun dura Anambra ana cikin zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami’an EFCC sun isa Anambra domin sa ido kan yiwuwar sayen kuri’u da kuma tabbatar da gaskiya zaben gwamna.

Kara karanta wannan

Anambra: An fadi yawan ƙananan hukumomi da Soludo ya lashe, ya nakasa APC

An hango jami’an EFCC sun isa makarantar firamare ta CPS da ke Amawbia, karamar hukumar Awka ta Kudu domin sa ido kan zaben da kuma hana sayen kuri’a.

Masu sa ido a zaben gwamnan Anambra sun koka kan yadda ake sayen kuri’a da sauran laifuffukan zabe da ke gudana a wasu rumfunan zabe na jihar.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com