Kebbi: Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Kubuta daga Hannun 'Yan Bindiga, an Ji Yadda Ya Tsira
- Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Samaila Bagudu ya shaki iskar 'yanci bayan kwashe wasu kwanaki a hannun 'yan bindiga
- Samaila Bagudu ya shiga hannun 'yan bindiga ne bayan sun yi awon gaba da shi jim kadan bayan kammala sallar Isha'i
- Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta tabbatar da kubutar da mataimakin shugaban majalisar dokokin a wata sanarwa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Kebbi, Muhammad Samaila Bagudo, ya shaki iskar 'yanci.
Muhammad Sama'ila Bagudu ya kubuta ne daga hannun ‘yan bindigan da suka yi awon gaba da shi.

Source: Facebook
Samaila Bagudu ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
Jaridar The Punch ta ce babban sakataren yada labaran gwamnan jihar Kebbi, Ahmed Idris, ya tabbatar da faruwar hakan a daren Asabar, 8 ga watan Nuwamban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ahmed Idris ya ce dan majalisar ya samu kubuta kuma an haɗa shi da iyalinsa cikin koshin lafiya.
An sace Samaila Bagudu ne da misalin karfe 8:20 na dare a ranar Alhamis, 31 ga watan Oktoba, 2025, a garinsa na Bagudu, hedikwatar karamar hukumar Bagudu, bayan ya kammala sallar Isha’i a masallaci.
Yan bindigan sun kai farmaki a garin, inda suka dauke shi zuwa inda ba a sani ba, lamarin da ya haifar da tashin hankali a tsakanin mazauna yankin.
Ko da yake ba a bayyana cikakken yadda aka sako shi ba, majiyoyi daga gwamnati sun tabbatar da cewa an sako shi ba tare da wani rauni ba.
'Yan sanda sun yi bayani
Tashar Channels tv ta ce jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi, CSP Nafiu Abubakar, ya tabbatar da ceto dan majalisar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
A cewarsa, an kai Samaila Bagudu asibiti don duba lafiyarsa sannan aka mayar da shi gida domin haɗuwa da iyalinsa.
Ya yabawa jajircewar jami’an tsaro da suka haɗa kai wajen aiwatar da aikin ceto da kuma goyon bayan da jama’ar jihar da suka bayar ta hanyar bada bayanai masu muhimmanci da suka taimaka wajen samun nasarar aikin.

Source: Original
“Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi za ta ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane, da sauran masu aikata laifuffuka."
"Ana kuma kira ga jama’a su kasance masu lura, su rika kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da shi ba ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko hukumomin tsaro don gaggawar daukar mataki.”
- CSP Nafiu Abubakar
'Yan sanda sun musanta kisan shugaban CAN
A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta yi martani kan rahotannin da ke cewa an kashe shugaban kungiyar CAN a jihar.
Ta bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a rahoton mai cewa an kashe shugaban ta hanyar fille masa kai.
Rundunar 'yan sandan ta bukaci jama'a da su yi watsi da rahoton tare da tabbatar da sahihancin kowane labarin kafin yada shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


