Yaran Bello Turji Sun Hallaka Jama’a a Sokoto, Sun Sace ’Yan Mata yayin Harin

Yaran Bello Turji Sun Hallaka Jama’a a Sokoto, Sun Sace ’Yan Mata yayin Harin

  • ’Yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun kai wani hari na musamman inda suka hallaka mutane da sace wasu da dama a Sokoto
  • Rahotanni sun ce mafi yawan mutanen da aka sace 'yan mata ne, yayin da mutum ɗaya ya jikkata sosai a harin da aka kai da dare
  • Mazauna yankin sun roƙi hukumomi su ƙara tsaro da sintiri, tare da ƙoƙarin ceto waɗanda aka sace daga hannun ’yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - ’Yan bindiga masu biyayya ga hatsabibin dan ta’adda, Bello Turji, sun kai hari a kauyen Bargaja, da ke karamar hukumar Isa ta Jihar Sokoto.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa maharan sun kashe mutum biyar tare da sace wasu tara yayin hari da ya tayar da hankulan mutane a yankin.

Kara karanta wannan

Abu ya tsananta: Mutane sun tsere daga gidajensu kan hare haren 'yan bindiga a Kano

Yaran Bello Turji sun kai hari a jihar Sokoto
Taswirar jihar Sokoto da ke da iyaka da Nijar. Hoto: Legit.
Source: Original

Yaran Bello Turji sun kai hari a Sokoto

Bakatsine mai kawo rahotanni kan matsalolin tsaro ya tabbatar da faruwar lamarin a shafinsa na X a yau Asabar 8 ga watan Nuwambar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin ya faru ne da daren Jumma’a, 7 ga Nuwamba 2025, lokacin da ’yan bindigar suka mamaye kauyen dauke da manyan makamai.

Rahoton ya bayyana cewa mafi yawancin mutanen da aka sace yayin harin yan mata ne masu kananan shekaru

“Dare jiya, ’yan bindiga masu biyayya ga Bello Turji sun shiga kauyen Bargaja a karamar hyujkumar Isa na Jihar Sokoto, inda suka kashe mutane da dama."

- Cewar sanarwar

Majiyoyi sun ƙara da cewa, mutum ɗaya ya jikkata sosai, yayin da aka sace akalla mutane 10, yawancinsu yan mata.

Ana zargin yaran Turji sun kai hari a Sokoto inda suke hallaka mutum 5
Ministan tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Sokoto: Abin da mazauna yankin ke bukata

Rahoton ya ce wannan sabon hari yana nuna ci gaba da barazanar ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

Yankin na daga wuraren da jama’a ke fuskantar hare-hare ba tare da wani gargaɗi ko kariya daga jami’an tsaro ba wanda ya ke jawo rasa rayukan mutane a kullum.

Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su ƙara yawan sintiri da kuma yin gaggawar kubutar da waɗanda aka sace daga hannun miyagun.

“Mutanenmu suna cikin tsaka mai wuya. Ba mu da kariya, kuma kowanne dare muna rayuwa cikin fargaba.”

- In ji wani mazaunin Bargaja

Har zuwa yanzu, jami’an tsaro ba su fitar da sanarwa ba game da harin, sai dai jama’a na fatan gwamnati za ta dauki mataki domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Bello Turji ya saki mutane 100 a Zamfara

Kun ji cewa majiyoyi sun tabbatar da cewa dan ta'adda, Bello Turji ya saki mutum sama da 100 da yake tsare da su a yankin Zamfara.

Rahoto ya ce hakan ya biyo bayan tattaunawa tsakanin jagoran ‘yan bindigar da shugabannin al’umma a jihar domin tabbatar da cewa an samu zaman lafiya a yankin.

Hukumomi sun ce suna sa ido sosai don tabbatar da cewa dan ta'addan bai sake daukar makami ba bayan sulhun wanda ake ganin zai iya haifar da 'da mai ido.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.