Shugaban Amurka, Trump ya Ga ta Kansa da 'Yan Shi'a Suka Fito Zanga Zanga a Jihar Kano

Shugaban Amurka, Trump ya Ga ta Kansa da 'Yan Shi'a Suka Fito Zanga Zanga a Jihar Kano

  • 'Yan shi'a sun yi fatali da barazanar shugaban Amurka, Donald Trump na kawo farmaki Najeriya domin yaki da yan ta'adda
  • Rahotanni sun nuna cewa Yan Shi'a sun fito zanga-zanga a titunan cikin birnin Kamo domin nuna adawa da ikirarin Trump
  • Sun zargi shugaban kasar Amurka da bullo da wannan hanyar domin raba kawunan musulmi da kiristoci a Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Mambobin Kungiyar Musulunci ta Najeriya (IMN), da aka fi sani da ’yan shi’a, sun gudanar da zanga-zanga a titunan birnin Kano a ranar Asabar, 8 ga watan Nuwamba, 2025.

Yan shi'a sun fantsama zanga-zanga ne don nuna adawa da furucin Shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya yi barazanar kawo farmaki Najeriya da nufin yaƙi da ’yan ta’adda.

Mabiya addinin shi'a.
Hoton yan shi'a yayin da suka fito zanga-zangar lumana a Kano Hoto: Na'im Yahaya Gafai
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa mabiya akidar shi'a sun gudanar da zanga-zangar cikin lumana, ba tare da tashin hankali ba.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da batun barazanar Trump, Tinubu ya gana da shugaban kasar Saliyo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda yan shi'a suka fito zanga-zanga

Dubban masu zanga-zangar sun yi tattaki a manyan hanyoyi cikin birnin Kano, dauke da fastoci da kwalaye masu dauke da sakonnin ƙaryata ikirarin Trump cewa ana kisan gillar Kiristoci a Najeriya.

An ga wasu daga cikin masu zanga-zangar suna jan tutar Amurka a kasa, yayin da wasu kuma suka rike hoton Trump a matsayin nuna fushi da abin da ya fada.

Tun farko Shugaba Trump ya sake sanya Najeriya a jerin kasashen da ake da babbar matsala kan yancin addini bisa zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Trump ya yi zargin cewa ana cin zarafin Kiristoci a Najeriya ta hannun kungiyoyin ta’addanci masu taattsauran ra'ayin islama.

Shugaban ya gargadi gwamnatin Najeriya da cewa idan ba ta dauki mataki ba, zai tura sojojin Amurka domin “dakatar da kisan.”

Kungiyar IMN ta musanta ikirarin Trump

A martaninsu, ’yan shi’a sun bayyana kalaman Trump a matsayin ƙarya, masu tayar da fitina, kuma masu haɗari ga zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya

A cikin wata sanarwa da Abdullahi Danladi na kungiyar IMN ya fitar, ya zargi kasashen Yamma da amfani da farfaganda wajen haddasa rabuwar kai tsakanin Musulmi da Kiristoci a Najeriya.

Danladi ya bayyana cewa kungiyarsu ta dade tana goyon bayan haɗin kai da zaman lafiya tsakanin al’umma, yana mai jaddada cewa matsalolin Najeriya ba na addini ba ne.

Yan kungiyar IMN.
Hoton yan shi'a yayin da suka fara zanga zanga a Kano Hoto: Naim Yahaya
Source: Facebook

'Yan shi'a sun soki yan siyasar Najeriya

Sai dai ya jingina wasu matsalolin da Najeriya ke fuskanta da rashawa, son kai, da rashin adalci daga shugabannin siyasa, cewar Daily Post.

"Addinin Musulunci da na Kirista dukkansu suna koyar da ɗabi’u iri ɗaya. Amma wasu ’yan siyasa da kasashen waje suna amfani da bambance-bambancenmu domin cimma muradunsu,” in ji Danladi.

AYDM ta gargadi gwamnoni 8

A wani labarin, kun ji cewa wata kungiyar yarbawa (AYDM) ta ja hankalin gwamnonin Kudu maso Yamma da na Kogi da Kwara kan barazanar da Amurka ta yi.

AYDM ta gargadi wadannan gwamnoni su shirya tunkarar tasirin abin da zai biyo baya idan gwamnatin Amurka ta kawo farmaki Najeriya.

AYDM ta ce irin wannan hari na iya tursasa ‘yan ta’adda barin Arewa su koma yankin Yammacin ƙasa, musamman idan Amurka ta kai musu farmaki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262