Malamin Addini Ya Gayawa Tinubu Gaskiya kan Mutanen da Ke Tare da Shi, Ya Ba Shi Shawara

Malamin Addini Ya Gayawa Tinubu Gaskiya kan Mutanen da Ke Tare da Shi, Ya Ba Shi Shawara

  • Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya soki wasu daga cikin masu ba Mai girma Bola Tinubu shawara
  • Fasto Enoch Adeboye ya nuna cewa wasu daga makusantan shugaban kasan ba sa sonsa saboda irin shawarwarin da suke ba shi
  • Babban faston ya koka da cewa wasu daga cikinsu na Shugaba Tinubu gurguwar shawara wadda ba za ta amfane shi ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye, ya yi magana kan masu ba Shugaba Bola Tinubu shawara.

Fasto Enoch Adeboye ya bayyana damuwa kan cewa Shugaba Tinubu yana samun gurguwar shawara daga wajen wasu daga cikin masu ba shi shawara.

Fasto Adeboye ya ba Shugaba Tinubu shawara
Shugaba Bola Tinubu da Fasto Enoch Adeboye Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Pastor E.A. Adeboye
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake wa’azi a taron addu’ar Holy Ghost na watan Nuwamba mai taken “The Eve of Glory".

Kara karanta wannan

'Abin da Rasha, China za su yi bayan harin Amurka': Malami ya gargadi Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban faston ya nuna damuwarsa kan wani jawabi da Tinubu ya yi, inda ya tabo batun tsaron kasa.

Me Adeboye ya ce kan Tinubu

Fasto Adeboye wanda ya ambaci shugaban kasan a matsayin surikinsa, ya koka kan jawabin Tinubu inda ya ce tsaro ya inganta kuma mutanen da suka rasa gidajensu sun koma kauyukansu.

“Na kusan yin magana a watan da ya gabata lokacin da na ji jawabi daga surikina, shugaban kasa. Za ku iya komawa ku saurari jawabin, musamman ɓangaren da ya shafi tsaro."
"Lokacin da na ji ya ce komai ya daidaita yanzu, kuma mutanen da aka raba da gidajensu sun koma kauyukansu, na kusan cewa wanda ya rubuta wa shugabana, surikina, wannan jawabi, bai son sa.”
“Kuma idan za ku tambaye ni, ‘To ai shugaban kasa ne ya karanta jawabin,’ zan ce, shin bai duba abin da aka rubuta masa ba ne kafin ya karanta?"
"Idan haka ne, to akwai mutane da yawa a kusa da surikina da ba sa gaya masa gaskiya. A washegarin ranar, mun karanta a jarida cewa an kashe wani basarake, ko dai a Kwara ko a Kogi.”

Kara karanta wannan

Fasto Adeboye ya kawo mafita, ya aika sako ga Shugaba Tinubu kan barazanar Amurka

- Fasto Enoch Adeboye

Sai dai, Adeboye ya ce yanzu ba lokacin dora laifi bane, domin matsalar tsaro ta samo asali ne tun kafin gwamnatin Tinubu, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar da labarin.

“Shugabanmu ya gaji wannan matsala, ta wanzu tun kafin shi. Amma ni a matsayina na masani a lissafi, abin da nake so shi ne mafita, ba dora laifi ba.”

- Fasto Enoch Adeboye

Fasto Adeboye ya soki masu ba Tinubu shawara
Shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye Hoto: Pastor E.A. Adeboye
Source: Facebook

Adeboye ya ba Tinubu shawara

Faston ya ba da shawarar cewa gwamnati ta nemi hanyar diflomasiyya don roƙon Shugaban Amurka Donald Trump da ya ba Najeriya kwanaki 100 na rangwame don a samu damar tsara dabarun yaki da ta’addanci.

“A kira shugabannin tsaro duk da cewa sababbi ne, a ce su yi abin da ya dace cikin wata uku ko su yi murabus."
“Mun dade muna yi wa Najeriya addu’a, ba zai yiwu mu yi waɗannan addu’o’i da yawa ba tare da ganin wani canji ba.”

Kara karanta wannan

Ana tsaka da batun barazanar Trump, Tinubu ya gana da shugaban kasar Saliyo

- Fasto Enoch Adeboye

Mukhtar Kabir ya goyi bayan kalaman da babban faston ya yi kan cewa mashawartan Tinubu ba sa gaya masa gaskiyar halin da ake ciki.

"Tabbas idan ka saurari sanarwowin da shugaban kasan yake fitarwa, za ka lura cewa kamar bai san abin da ke faruwa a kasa."
"Har yanzu akwai matsalar rashin tsaro, amma idan ka saurari bayanansa sai ka ji yana cewa al'amura sun gyaru."
"Tabbas ina ganin cewa mashawartan ba sa gaya masa gaskiya, kuma hakan abu ne mai hadari."

- Mukhtar Kabir

​Tinubu ya gana da Sarkin Musulmi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Mai girma Tinubu ya gana da sarkin musulmin ne a fadar shugaban kasa da ke fadar Aso Rock a birnin Abuja.

Ganawar na cikin jerin tattaunawa da neman shawarwari da Shugaba Tinubu ke yi da shugabannin addini da na gargajiya a Najeriya kan barazanar da Amurka ta yi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng