Turkiyya na Neman Kama Netanyahu da Manyan Sojojin Isra'ila kan Kisa a Gaza

Turkiyya na Neman Kama Netanyahu da Manyan Sojojin Isra'ila kan Kisa a Gaza

  • Gwamnatin Turkiyya ta bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, bisa tuhumar kisan kare-dangi a Gaza
  • Hukumar kula laifuffuka ta Istanbul ta ce akwai mutane 37 da ake zargi, ciki har da ministoci da manyan hafsoshin sojan Isra’ila
  • Isra’ila ta mayar da martani da cewa wannan mataki na urkiyya ba komai ba ne face wani salon siyasa daga Shugaba Reccap Erdogan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Turkey – Gwamnatin Turkiyya ta sanar da bayar da sammacin kama Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, tare da wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Rahotanni sun nuna cewa an nemi kama su ne bisa zargin aikata kisan kare-dangi da laifuffukan yaƙi a yankin Gaza tun watan Oktoban 2023.

Erdogan, Benjamin Netanyahu
Shugaban Turkiyya, Erdogan da Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Al-Jazeera ya ce hukuncin ya fito ne daga ofishin mai gabatar da kara na Istanbul a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

Trump: Sojojin Amurka sun dura a Rivers? Fadar shugaban kasa ta magantu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an Isra'ila da ake nema a kama

Bayan Netanyahu, hukuncin ya hada da ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz; ministan tsaron cikin gida, Itamar Ben-Gvir.

Indian Express ta rahoto cewa babban hafsan sojoji, Laftanar Janar Eyal Zamir na cikin jerin mutane 37 da ake zargi da laifuffuka masu tsanani.

Turkiyya ta ce wadannan jami’an sun aikata kisan kare-dangi da kuma laifuffukan cin zarafin bil’adama da Isra’ila ta kaddamar kan Palasdinawa tun lokacin da rikici ya barke a Gaza.

Wasu laifuffukan da aka ce Isra'ila ta yi

A cikin sanarwar, Turkiyya ta kawo wasu manyan laifuffuka da Isra’ila ta aikata, ciki har da harin da aka kai a ranar 17 ga Oktoba, 2023, kan Asibitin al-Ahli Baptist, wanda ya kashe mutum 500.

Haka kuma ta zargi dakarun Isra’ila da lalata kayayyakin asibiti a ranar 29 ga Fabrairu, 2024, tare da hana shigar da kayan agaji ga mutanen Gaza.

Kara karanta wannan

Lamari ya girma: Amurka ta soke bizar mutane 80,000, ciki har da 'yan Najeriya

Isra'ila ta ruguza Gaza.
Wani gini da Isra'ila ta rusa a Gaza. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sanarwar ta kuma ambaci asibitin “Turkish-Palestinian Friendship” da gwamnatin Turkiyya ta gina a Gaza, wanda Isra’ila ta kai wa hari.

Martanin kasar Isra’ila da Hamas

Ministan harkokin wajen Isra’ila, Gideon Saar, ya yi martani, inda ya bayyana matakin na Turkiyya a matsayin “wasan siyasa” da “shirin bata suna” daga Shugaba Recep Tayyip Erdogan.

Ya ce:

“Isra’ila ta nuna kin amincewa da wannan wasan siyasa da sabon zaluncin Erdogan.”

Sai dai kungiyar Hamas ta bayyana godiya ga Turkiyya bisa wannan mataki, tana cewa:

“Turkiyya ta sake tabbatar da matsayinta na gaskiya, adalci da ‘yan uwantaka da ta daɗe tana nuna wa al’ummar Falasdinawa da aka zalunta.”

A halin yanzu, rahotanni daga Gaza sun nuna cewa yakin Isra’ila ya yi sanadin mutuwar Palasdinawa 68,875 tare da raunata sama da 170,000 tun daga watan Oktoba 2023.

Maganar Trump kan harin Isra'ila a Iran

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban Amurka ya bayyana cewa shi da kansa ya jagoranci harin da Isra'ila ta kai Iran.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Ƴan bindiga sun farmaki dan majalisar Neja, an kashe jami'an tsaro

Trump ya ce yana sane da matakin da Benjamin Netanyahu ya dauka, kuma sun yi barna sosai a harin.

A karon farko bayan kai harin, kasar Amurka ta ce bata da hannu a farmakin kafin Trump ya fito da bayani sabanin haka.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng