Rashin Tsaro: Gwamna Uba Sani Ya Aika Sakon Gargadi ga 'Yan Siyasa

Rashin Tsaro: Gwamna Uba Sani Ya Aika Sakon Gargadi ga 'Yan Siyasa

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya yi tsokaci kan wani halin da wasu 'yan siyasa ke nunawa dangane da matsalar rashin tsaro
  • Mai girma Uba Sani ya bayyana cewa kuskure ne a rika siyasantar da matsalar rashin tsaro domin cimma wasu manufofi
  • Ya soki 'yan siyasan da ke kokarin bata sunan kasa, wadanda ya ce da wata rigima ta balle za su kwashe kayansu su tafi kasashen waje

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira da babbar murya ga 'yan siyasa kan matsalar rashin tsaro.

Gwamna Uba Sani ya shawarci ‘yan siyasa da su bambance tsakanin sukar gwamnati ta hanyar gina kasa da kuma ayyukan da ke iya lalata haɗin kan Najeriya da zaman lafiyarta.

Uba Sani ga ja kunnen 'yan siyasa kan rashin tsaro
Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar bayan ziyarar da daraktocin hukumar DSS suka kai masa a ranar Juma'a, 7 ga watan Nuwamban 2025.

Kara karanta wannan

Sokoto: Gwamnati ta musanta sakaci kan harin 'yan bindiga, ta bayya yadda lamarin yake

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Uba Sani ya ce kan 'yan siyasa?

Gwamnan wanda ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kasance masu kishin kasa, ya gargadi ‘yan adawa da su guji yin amfani da batutuwan tsaro wajen neman riba ta siyasa ko ta kashin kai.

Ya jaddada cewa kasar Najeriya ta fi kowanne dan kasa muhimmanci, rahoton ya zo a jaridar The Punch.

Gwamna Uba Sani ya nuna damuwa kan halayen wasu ‘yan siyasa da ke amfani da sunan adawa da manufofin gwamnati wajen bata sunan kasa a kafafen yada labarai, yana mai cewa hakan ba tsarin dimokuradiyya ba ne.

“Wasu ‘yan siyasa suna manta cewa wa'adin masu rike da mukaman siyasa yana karewa, amma Najeriya za ta ci gaba da kasancewa."
“Za ka iya sukata a matsayina na gwamna, amma idan ka yi abin da ya haifar da rikici, ya bata sunan kasa ko tayar da hankali a jihar Kaduna, to kai mai son cin ribar rikici ne."

Kara karanta wannan

'Farashin abinci ya kara yin kasa warwas a Najeriya', Minista ya bayyana dalili

- Gwamna Uba Sani

Uba Sani ya soki 'yan siyasa

Ya kuma ce da yawa daga cikin ‘yan siyasar da ke cikin adawa a yanzu ba su cikin gwagwarmayar da aka yi da mulkin soja ko yakin neman dimokuradiyya a baya.

“Wasu daga cikin ‘yan manya suna amfani da matsayinsu wajen lalata tsaron talakawa, alhali ba su damu da abin da zai faru ba a kasar."
“Idan wani abu ya faru, wadanda ke zaune a GRA, ‘ya’yansu kuma suna kasashen waje, za su iya guduwa. Amma talakawa da marasa galihu su ne za su sha wahala.”

- Gwamna Uba Sani

Gwamna Uba Sani ya ja kunnen 'yan siyasa
Sanata Uba Sani na jawabi a wajen wani taro Hoto: @ubasanius
Source: Facebook

Gwamnan ya yi Allah-wadai da ‘yan siyasa da ke tayar da zanga-zanga daga cikin gidajensu, alhali ‘ya’yansu suna rayuwa cikin jin dadi a kasashen waje.

“Abin da ke nufin cutar da kasarka da sunan adawa ba kishin kasa ba ne, laifi ne. Waɗannan su ne dabarun masu son kawo rikici."

- Gwamna Uba Sani

Kara karanta wannan

Rikici tsakanin lauya da Sheikh Gumi ya canja salo, ana shirin dangana wa ga kotu

Saida Nasir ta shaidawa Legit Hausa cewa tabbas abin da wasu 'yan siyasa ke yi kan rashin tsaro ba daidai ba ne.

Ta bayyana cewa wasu 'yan siyasan har kosawa suke a kai hari domin su samu bakin sukar gwamnati.

"Tabbas tsaro abu ne da ya shafi kowa, amma kuskure a rika shigo da siyasa a ciki. Ko kadan abin da za a sanyawa siyasa ba ne."

- Saida Nasir

Gwamnatin Uba Sani ta kubutar da mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, ta samu nasarar ceto wasu mutanen da 'yan bindiga suka sace.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta samu nasarar kubutar da mutane fiye da 500 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su.

Ta ce ta yi amfani da sabon tsarin samar da zaman lafiya wanda bai shafi biyan kudin fansa ko amfani da karfin makami kan 'yan bindiga ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng