Matatar Dangote Ta Rage Farashin Litar Man Fetur daga N877 a Najeriya

Matatar Dangote Ta Rage Farashin Litar Man Fetur daga N877 a Najeriya

  • Matatar Dangote ta rage farashin litar man fetur daga N877 zuwa N828, abin da ke nufin saukar kashi 5.6 cikin 100
  • Sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar Juma’a, bisa sabon jadawalin farashi da aka fitar daga matatar Dangote
  • Farashin ya sauka ne a lokacin da ake fuskantar hauhawar kudin ma'aikata da karuwar farashin dizal da man jiragi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur daga N877 zuwa N828 a kowace lita daga ranar Juma'a.

Saukar farashin ya zo ne bayan lokaci da matatar ta dauka bata yi irin wannan sauyin ba domin daidaita farashin cikin gida da yanayin kasuwar duniya.

Matatar Dangote
Aliko Dangote da sashen matatarsa. Hoto: Dangote Industries
Source: Getty Images

Bisa bayanan da shafin Petroleumprice.ng ya fitar, sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar Juma’a, 7 ga Nuwamba, 2025.

Kara karanta wannan

"Ba don kiristoci ba ne," An jero abubuwa 3 da suka harzuka Amurka ta fara shirin kawo hari Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon farashin fetur a matatar Dangote

Wani dillalin man fetur ya tabbatar wa Punch cewa an samu sauki a farashin litar man fetur a matatar Dangote:

“Matatar Dangote ta rage farashin daga N877 zuwa N828 a kowace lita,”

Ya kara da cewa matakin na iya kawo saukin farashin fetur a gidajen mai a wasu jihohi nan gaba kadan.

Legit Hausa ta gano cewa rage kudin lita daga N877 zuwa N828 zai samar da saukin N49 ga masu sayen mai a matatar.

Sabon farashin Dangote da tasirinsa

Majalisar manyan masu kasuwancin makamashi (MEMAN) ta tabbatar da saukar farashin a rahotonta na yau da kullum, inda ta ce matakin zai taimaka wajen daidaita farashi a kasuwanni.

Sai dai rahoton ya nuna cewa, yayin da farashin fetur ya dan sauka, sauran nau’ukan mai kamar dizal da man jiragen sama sun kara tashi.

Gidan mai a Najeriya
Mutane ne na sayen fetur a gidan mai. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangane da binciken da aka gudanar a kasuwar masu dakon mai, kamfanin MRS Oil na ci gaba da sayar da man fetur a N870, wasu kuma ba su sauke farashinsu ba har yanzu.

Kara karanta wannan

'Yan kasuwar man fetur sun ce farashi zai hauraN1000 da Tinubu ya kawo haraji

Farashin dizal da man jirgin sama

Duk da saukar da farashin man fetur da matatar Dangote ta yi, rahotanni sun tabbatar da cewa an samu karin farashin dizal a kasuwar cikin gida.

An ruwaito cewa dizal yana kan N784.75 a tashoshin bakin teku, yayin da farashin ya kai N950.00 a kowace lita a matatar Dangote.

Haka kuma, man jiragen sama ya tashi zuwa N815.50, da N1,025.77 a kowace lita a wajen manyan diloli.

Sai dai gas (LPG) ya tsaya daram a N15,000, wanda shi ne kadai nau’in mai da bai samu canjin farashi ba duk da matsin kasuwa.

Ana maganar sayar da matatun Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta sake magana game da yiwuwar sayar da matatun man fetur da ta mallaka.

Hakan na zuwa ne bayan matatun Warri, Fatakwal sun gaza fara aiki yadda ya kamata duk da gyara da aka musu.

A kwanakin baya, Alhaji Aliko Dangote ya ce ba zai saye matatun ba a lokacin da ake masa tambayoyi a jihar Legas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng