"Ba don Kiristoci ba ne," An Jero Abubuwa 3 da Suka Harzuka Amurka Ta Fara Shirin Kawo Hari Najeriya
- Ana zargin cewa kisan kiristoci ba shi ne asalin dalilin da ya sa kasar Amurka ke kokarin kawo farmaki Najeriya ba
- Farfesa Lai Olurodeya ya bayyana abubuwa uku ciki har da matatar Dangote a matsayin wadanda Amurka ke jin haushi
- Tsohon malami a jami'ar UNILAG ya bukaci manyan Najeriya su hada kai wajen kare kasarsu daga masu tsoma baki daga ketare
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Farfesa Lai Olurode, tsohon malamin ilimin zamantakewa a Jami’ar Legas (UNILAG), ya yi fashin baki kan barazanar da Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi wa Najeriya.
Olurode ya bayyana cewa ko kadan ba don kare rayukan kiristoci Shugaba Trump ya yi barazanar kawo farmaki Najeriya ba, sai don wasu dalilai daban.

Source: Getty Images
Premium Times ta ce a cikin wata sanarwa da aka raba wa manema labarai, Farfesa Olurode ya bayyana cewa ikirarin Trump “wani makirci ne da ke ɓoye ainihin manufarsa.”
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya fara shawo kan matsalar tsaro
Ya ce Trump na kokarin turo sojojin Amurka su kawo hari Najeriya ne saboda nuna wariyar launin fata, siyasa da manufofin tattalin arziki.
Farfesa Olurode ya ce:
“Najeriya ta jima tana fama da hare-haren yan ta'adda, waɗanda ke kai hari ga sojoji, gine-ginen gwamnati, kadarorin tattalin arziki da wuraren ibada na Musulmi da Kirista.
“Kusan babu wata jiha da ba ta fuskanci irin wannan tashin hankali ba, amma a ƙarƙashin wannan gwamnati, akwai alamun raguwar ayyukan ta’addanci.”
Tsohon kwamishina INEC ya ce, shirin Trump game da Najeriya da sauran ƙasashen baƙar fata na nuna dogon tarihin wariyar launin fata da ke cikin siyasar Amurka.
“Tun kafin ya zama shugaban ƙasa, Trump ya nuna ƙiyayya ga bakaken Amurkawa da sauran mutanen da ba fararen fata ba,” in ji Farfesa Olurode.
Abubuwan da shugaban Amurka ke jin haushi
Farfesan ya kuma danganta matsayar Trump da rashin jin daɗin Amurka kan ci gaban masana’antar mai a Najeriya, musamman bayan bude matatar mai ta Dangote.

Kara karanta wannan
Kisan kiristoci: Yan Majalisa 31 sun goyi bayan matakin da Amurka ta dauka kan Najeriya
“A karon farko a tarihinmu, muna tace mai da kanmu. Wannan ya rage dogaro da Amurka wajen aiki da jiragen ruwa da matatun mai. Wannan ci gaban yana damun su."
“Kamar yadda Walter Rodney ya bayyana a cikin How littafin Europe Underdeveloped Africa, Turawan yamma ba sa son Afrika ta dogara da kanta.”
A ɓangaren siyasa da al’adu, Farfesan ya ce, karuwar kimar Najeriya a duniya, musamman ta hanyar al’adu da mazauna kasashen waje ke nuna wa, na damun wasu ‘yan Amurka ciki har da Trump.

Source: Twitter
Farfesa Olurode ya ba Najeriya shawara
Yayin da yake sukar kalaman Trump da ya kira “masu tayar da fitina da haɗari,” Farfesa Olurode ya shawarci gwamnatin Tinubu ta zama mai natsuwa, diflomasiyya da dabaru wajen mayar da martani.
A ƙarshe, ya kira ‘yan siyasa da masu ilimi a Najeriya su haɗa kai wajen kare martabar ƙasarsu da ‘yancinta daga tsoma bakin kasashen waje, cewar rahoton Guardian.
Sanata Barau ya caccaki Trump
A baya, kun ji labarin cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi martani mai zafi ga Shugaban Amurka, Donald Trump.
Ya ce Najeriya ba za ta lamunci raini daga kowace ƙasa ba, inda ya ayyana maganganun Trump a matsayin na rashin mutunci kuma sum sabawa ƙa’idojin diflomasiyya.
Sanata Barau ya yi kira ga Trump da ya janye maganarsa tare da ba da haƙuri ga al’ummar Najeriya saboda rashin mutunta ta da ya yi a idon duniya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

