'Abin da Zan Faɗawa Trump Ido da Ido, idan Na Haɗu da Shi': Barau Jibrin Ya Fusata
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya sake yin magana cikin fushi game da barazanar Donald Trump
- Sanata Barau Jibrin ya caccaki Trump bisa kalamansa kan Najeriya, yana mai cewa sun sabawa dokokin kasa da kasa
- Ya bukaci Trump ya janye kalamansa tare da ba da haƙuri ga ‘yan Najeriya, yana mai jaddada cewa ƙasar ba za ta tsorata ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi kaca-kaca da Shugaban Amurka, Donald Trump.
Sanata Barau ya dura kan Trump ne bisa kalamansa da barazanar da ya yi wa Najeriya a karshen watan Oktobar 2025.

Source: Twitter
A wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta wanda Tribune ta gano, Barau ya ce Najeriya ba za ta lamunci raini daga kowace ƙasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Barazanar da Donald Trump ya yi ga Najeriya
A nasa ɓangaren, Trump ya bayyana cewa addinin Kiristanci na cikin haɗari a Najeriya, inda ya zargi gwamnati da kasa kare mabiya addinin.
Ya ce an kashe dubban Kiristoci a Najeriya, yana zargin ‘yan ta’addan Musulmi da kisan gilla.
Trump ya gargadi gwamnati cewa Amurka za ta iya tsoma baki da karfi idan har kashe-kashen suka ci gaba.
Ya kuma sanar da cewa ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka ta fara shirin daukar mataki kan ‘yan ta’addan da ke kisan Kiristoci, yana mai cewa Amurka “za ta kare Kiristoci a ko’ina cikin duniya.”

Source: Facebook
Sanata Barau ya yi wa Trump martani
Sai dai Barau bai ji dadin haka ba inda ya ayyana maganganun Trump a matsayin “na rashin mutunci” kuma suka sabawa ƙa’idojin diflomasiyya da dokokin kasa da kasa.
Barau ya jaddada cewa Amurka dole ta mutunta ikon ƙasashe masu cin gashin kansu ba kawai ta rika yi wa mutane hawan kawara ba.
Ya kuma ce Trump ya yi abin kunya da ya kira Najeriya da munanan sunaye wanda ya zubar mata kima matuka, cewar BusinessDay.
Shawarar da Barau ya ba Donald Trump
Sanata Barau ya yi kira ga Trump da ya janye maganarsa tare da ba da haƙuri ga al’ummar Najeriya saboda rashin mutunta ta da ya yi a idon duniya.
“Abin da ya kamata shi ne a bi hanyar doka, a kai maganar Majalisar Ɗinkin Duniya."
- Sanata Barau Jibrin
Sanatan ya ƙara da cewa da Trump yana nan a wurin, da zai faɗa masa kai tsaye cewa matakinsa ba daidai ba ne kuma bai bi hanyar da ta dace ba.
Trump: Barau ya yi cacar baki da Akpabio
Mun ba ku labarin cewa an samu hatsaniya a zauren majalisa yayin da mataimakin shugaban majalisar, Jibrin Barau, ya kalubalanci Godswill Akpabio.
Sabanin ya biyo bayan maganganun shugaban kasar Amurka, Donald Trump, da ya zargi Najeriya da kisan gilla kan Kiristoci.
Akpabio ya ce majalisar ba za ta ce uffan ba sai gwamnati ta turo da takarda, amma Barau ya dage cewa ba ya jin tsoron Trump.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

