‘Ba Fulani Ke Yi ba’: An Gano Wadanda Ke Kashe Al’umma a Kudancin Najeriya
- Wani dan gwagwarmaya ya kare Fulani a jihar Anambra bayan kashe-kashe da aikata laifuffuka da ake yi a yankin
- Kwamred Osita Obi ya ce yawanci a jihar da yankin Kudu maso Gabas ‘yan gida ne ke aikata laifuffuka, ba baki daga waje ba
- Obi ya bukaci sarakunan gargajiya, shugabannin kananan hukumomi da jama’a su daina kare masu laifi domin dawo da zaman lafiya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Awka, Anambra - Mai kafa ƙungiyar 'Recover Nigeria Project', Kwamred Osita Obi, ya yi magana kan aikata laifuffuka a jihar Anambra.
Obi ya bayyana cewa mafi yawan laifuffuka da ake aikatawa a jihar Anambra da yankin Kudu maso Gabas ‘yan asalin yankin ne ke aikatawa, ba baki daga waje ba.

Source: Original
Tsaro: Dan gwagwarmaya ya zargi jami'an gwamnati
Obi ya bayyana haka a wata hira da jaridar Vanguard, inda ya ce rashin tsaro a yankin na ci gaba ne saboda wasu manyan jami’an gwamnati da na tsaro suna amfana.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan gwagwarmayar ya ce babu wata al’umma a Anambra ko yankin Igbo da ba ta san masu laifin da ke cikinta ba.
A cewarsa:
“Ba za ka samu wata al’umma a Anambra da ba ta san ‘yan ta’adda a cikinta ba. Har a garina akwai masu laifi, kuma kowa ya san su.”
Ya kara da cewa wasu jami’an gwamnati da ‘yan sanda suna amfana daga rashin tsaro."

Source: Facebook
Anambra: An wanke Fulani kan matsalar tsaro
Obi ya ce kare masu laifi a matakin al’umma yana hana gwamnati da hukumomin tsaro cimma nasarar da ke neman kawo zaman lafiya.
Ya kuma nuna damuwa kan yadda ake saki wadanda aka kama bayan an mika su ga jami’an tsaro, lamarin da ke barazana ga wadanda suka tona asirinsu.
“Idan muna boye masu laifi a tsakaninmu, me gwamnati za ta iya yi, idan na mika mai laifi ga ‘yan sanda, amma gobe a sake shi, me ya rage min?”

Kara karanta wannan
Zargin bai wa 'yan ta'adda kudi: Gwamnatin Kaduna ta fadi yadda ta taimaki 'yan bindiga
Obi ya jaddada cewa zaman lafiya ba zai dawo ba har sai sarakunan gargajiya, shugabannin kananan hukumomi da al’umma gaba ɗaya sun hada kai wajen fallasa masu aikata laifuka.
Ya ce ba gaskiya ba ne cewa Hausawa da Fulani ne ke haddasa matsalar tsaro, yana mai cewa mafi rinjaye daga cikin masu laifi ‘yan gida ne.
“A gaskiya, Hausawa-Fulani ba su fi kashi biyu cikin 100 ba, sauran laifukan kashi 98 cikin 100 ‘ya'yanmu ne, ‘yan Igbo.”
- Osita Obi
Obi ya bukaci jama’a da jami’an tsaro su rungumi gaskiya da amana domin dawo da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabas.
Gwamnan Anambra ya wanke Fulani kan rashin tsaro
A baya, kun ji cewa Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya fallasa wadanda ke assasa rashin tsaro da yayi kamari a jiharsa.
Soludo ya bayyana cewa, kashi 100 na wadanda aka kama sun garkuwa da mutane da kisa duk 'yan kabilar Igbo ne.
Yace babu wani cewa ba a san masu laifukan yankunan Kudu maso Gabas ba, ana kama su kuma duk matasan Igbo ake kamawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
