Babbar Magana: An Ruguza Ofishin Yakin Neman Zaben Bola Tinubu a Benue

Babbar Magana: An Ruguza Ofishin Yakin Neman Zaben Bola Tinubu a Benue

  • Hukumar raya birane ta jihar Benue ta rusa wani bangare na ofishin yakin neman zaben Shugaba Bola Tinubu da ke Makurdi
  • Masu goyon bayan Tinubu sun bayyana hakan a matsayin mataki maras hujja, suna masu cewa su na da lasisin mallakar filin
  • Gwamnatin jihar Benue ta musanta cewa siyasa ce ta haddasa hakan, ta kuma bayyana dalilin daukar matakin rusa ofishin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Benue – Hukumar raya birane ta jihar Benue ta rusa wani bangare na ofishin yakin neman zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ke tsakiyar birnin Makurdi.

Lamarin da ya tayar da kura tsakanin masu goyon bayan shugaban kasa da gwamnatin jihar kafin daga bisani a samu karin bayani.

Ofishin shugaba Tinubu a Benue
Wani sashe na ofishin Bola Tinubu da aka rusa a Benue. Hoto: Elizabeth Jessica
Source: Facebook

Punch ta rahoto cewa ginin da aka rusa shi ne ofishin kungiyar masu goyon bayan Ahmed Bola Tinubu, wanda kuma ke aiki a matsayin cibiyar kungiyar a jihar Benue.

Kara karanta wannan

'An rasa jigo a Najeriya,' Tinubu kan rasuwar tsohon gwamna, Janar Mohammed

An bayyana cewa jami’an hukumar sun rusa katangar ofishin ne a ranar Alhamis, mako guda bayan kaddamar da ofishin cikin wani biki da magoya baya daga jihohin Arewa ta Tsakiya suka halarta.

Martanin magoya bayan Bola Tinubu

Shugaban kungiyar masu goyon bayan Tinubu, Dr Tarnongo Simon, ya bayyana cewa babu dalilin rusa ofishin kuma abin takaici ne.

Ya ce:

“Mun zo ofishin da safe domin ci gaba da aiki, sai wadannan mutanen suka bayyana suka fara rushe ginin, ba tare da wani bayani ba.”

Simon ya ce ofishin yana da sahihin lasisin mallaka da kuma amincewar hukumar raya birane ta jihar Benue, yana mai tambayar dalilin da yasa aka musu haka.

Ya kara da cewa:

“Wannan mataki abin Allah wadai ne, amma ba zai raunana jajircewarmu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da burinmu na karfafa Arewa ta Tsakiya ba.”

Martanin gwamnatin jihar Benue

Sai dai gwamnatin jihar Benue ta musanta zargin cewa siyasa ce ta jawo rusa ginin, tana mai cewa aikin shimfida sabuwar hanya ce ta tilasta hakan.

Kara karanta wannan

Rikicin manoma da makiyaya: Mutane sun mutu a harin ramuwar gayya a Benue

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Kula Tersoo, ya fitar a Facebook, gwamnati ta ce gwamna Hyacinth Alia ba shi da hannu a rusau din.

Sanarwar ta bayyana cewa gine-ginen da ke kan layin aikin titin Wurukum–Yaikyor–Apir–Ikpayongo an rusa su ne domin shimfida sabuwar hanya ta Makurdi–Enugu da gwamnatin tarayya ke yi.

Gwamna Alia
Gwamna Alia na jihar Benue a ofis. Hoto: Kula Tersoo
Source: Facebook

Tersoo ya ce an tantance kadarorin da abin ya shafa, inda masu gine-ginen da ke da lasisi suka karbi diyya, yayin da aka umarci wadanda suka yi gini ba tare da izini ba su rushe nasu.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Abin ya zama rashin gaskiya ga duk wanda aka umarta da rushe gini saboda aikin gwamnati, sai ya fente wurin da launin siyasa ko ya saka hoton shugaba domin tada jijiyoyin wuya.”

Trump: APC ta kare Tinubu kan tsaro

A wani labarin, mun rahoto muku cewa jam'iyyar APC reshen Amurka ta rubuta wa majalisar Amurka wasika game da barazanar Donald Trump ga Najeriya.

Jam'iyyar ta bayyana cewa zargin da ake yi game da yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya ba gaskiya ba ne.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta kaddamar da bincike kan wasu ayyukan da Buhari ya yi

APC ta kara da cewa Bola Tinubu ya tashi tsaye wajen kare dukkan 'yan Najeriya, kuma ya ziyarci jihar Benue lokacin da aka kashe mutane da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng