Zaben Gwamna: Gwamnatin Jihar Anambra Ta Ayyana Ranar Hutu

Zaben Gwamna: Gwamnatin Jihar Anambra Ta Ayyana Ranar Hutu

  • Ana ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da ke yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
  • Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Chukwuma Soludo ta ayyana ranar hutu domin ba ma'aikata damar zuwa yankunansu domin su kada kuri'unsu
  • A cikin sanarwar da aka fitar, an bukaci ma'aikatan da su bada irin ta su gudunmawar wajen inganta tsarin dimokuradiyya

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Anambra - Gwamnatin jihar Anambra karkashin jagorancin Gwamna Chukwuma Soludo, ta ayyana ranar hutu domin zaben gwamnan da za a gudanar.

Gwamnatin ta ayyana ranar Jumma’a a matsayin rana ta hutu ga ma’aikatan gwamnati kafin zaben gwamnan jihar da za a gudanar a ranar Asabar mai zuwa.

Gwamnatin Anambra ta ayyana ranar hutu
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo Hoto: Prof Chukwuma Soludo
Source: Facebook

An bada hutu a jihar Anambra

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugabar ma'aikatan jihar Anambra, Theodora Igwegbe, ta fitar.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Dalilai 4 da za su sanya dan takarar APGA ya lashe zaben gwamna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Theodora Igwegbe ta fitar da sanarwar ne a ranar Alhamis, 6 ga watan Nuwamban 2025 a birnin Awka, babban birnin jihar Anambra.

Shugabar ma'aikatan ta ce an amince da ranar hutun ne bayan umarnin da Gwamna Chukwuma Soludo ya bayar domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar tafiya zuwa yankunansu domin su kada kuri'unsu a zaben.

Gwamnati ta bukaci ma'aikata su fito zabe

Ta bayyana cewa wannan matakin da gwamnan ya dauka, na nufin karfafa gwiwar ma’aikatan gwamnati domin su shiga cikin zaben a dama da su, rahoto ya zo a jaridar The Punch.

A cewarta, zabe nauyi ne da ya rataya a wuyan ’yan kasa, kuma ma’aikatan gwamnati na da gudunmawar da za su bada wajen inganta shugabanci nagari da tsarin dimokuradiyya.

Shugabar ma’aikatan ta kuma umarci dukkan masu rike da mukaman siyasa, manyan sakatarori da shugabannin ma’aikatu, hukumomin gwamnati su sanar da ma’aikatansu kuma su tabbatar da cewa an bi umarnin da gwamnan ya bada.

Kara karanta wannan

Jihohin da APC da PDP ke mulki a Najeriya kafin zaben gwamnan Anambra na 2025

Karanta wasu labaran kan jihar Anambra

Gwamnatin Anambra bada hutu saboda zaben gwamna
Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra Hoto: Prof Chukwuma Soludo
Source: Facebook

'Yar takarar gwamna ta yi wa ma'aikata alkawari

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yar takarar gwamnan jihar Anambra ta jam'iyyar AAC, Chioma Ifemeludike, ta yi alkawarin inganta walwalar ma’aikata.

Chioma Ifemeludike ta yi alkawarin karawa ma'aiata mafi karancin albashi zuwa N100,000 idan ta lashe zaɓen wanda za a gudanar da a ranar Asabar, 8 watan Nuwamban 2025.

'Yar takarar gwamnan ta ce gwamnatinta na da shirin zuba jari a fannonin koyar da sana’o’i da horar da matasa kan kasuwanci, domin su samu damar ginawa da kula da nasu kasuwancin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng