Jami'an Tsaro Sun Cafke Wata Mata Mai Safarar Makamai ga 'Yan Bindiga a Zamfara
- Dubun wata mata mai dauke da harsasai ta cika a jihar Zamfara bayan ta shiga hannun jami'an hukumar hana sha fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA)
- Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke matar ne dauke da kayan laifin wadanda ake zargin ta shirya kai su ga 'yan bindiga da ke cikin daji
- Shugaban karamar hukumar da aka cafke matar, ya yabawa jami'an tsaro bisa namijin kokarin da suka yi wajen kama ta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wata mata dauke da harsasai a jihar Zamfara.
Jami'an na NDLEA sun cafke matar ne a karamar hukumar Tsafe, dauke da harsasa da za a kai wa 'yan bindiga.

Source: Original
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mata mai safarar makamai ta shiga hannu
Jami'an na hukumar NDLEA sun cafke matar ne a yayin da suke binciken ababen hawa a kan titin Tsafe–Gusau ranar Laraba, 5 ga watan Nuwamban 2025.
Matar wacce ba a bayyana sunanta ba, ana zargin ta da niyyar kai harsasan ga ‘yan bindiga da ke ɓoye a dazukan jihar.
An ce ta fito ne daga karamar hukumar Birnin Magaji, inda aka gano harsasan a cikin kayanta lokacin da jami’an NDLEA suka dakatar da ita domin bincike.
An yabawa jami'an hukumar NDLEA
Shugaban karamar hukumar Tsafe, Malam Garba Shehu, ya tabbatar da kama matar, yana mai yabawa jami’an NDLEA bisa kokarin da suka yi wajen hana makamai kai wa hannun masu aikata laifi.
“Ina godiya ga jami’an NDLEA saboda jajircewarsu. Wannan kamun babban ci gaba ne wajen dakile yaduwar makamai da kayan da ke taimaka wa masu aikata laifuffuka a jihar Zamfara."

Kara karanta wannan
Tashin hankali: An kama bindigogi da mugayen makamai ana shirin shiga da su Zamfara
- Malam Garba Shehu
Ya kara da cewa gwamnatin karamar hukumar za ta ci gaba da ba da dukkan goyon baya da ake bukata ga jami’an tsaro, tare da gargadin cewa duk wanda aka kama yana taimaka wa ‘yan ta’adda zai fuskanci hukunci mai tsanani.
“Za mu ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro don su gudanar da aikinsu yadda ya kamata. Babu wanda zai tsira idan aka kama shi yana taimaka wa masu tada zaune tsaye."
- Malam Garba Shehu

Source: Twitter
'Ana ci gaba da bincike' - NDLEA
NDLEA ta tabbatar da cewa an mika matar da aka kama zuwa wata cibiyar tsaro domin ci gaba da bincike, yayin da hukumomin tsaro ke kara kaimi wajen bincike kan inda harsasan suka fito da kuma wadanda aka yi niyyar mika su a hannunsu.
Karamar hukumar Tsafe da makwabtanta suna daga cikin wuraren da hukumomin tsaro ke aiwatar da aikace-aikacen dakile hanyoyin samar da makamai da kayayyakin aiki ga ‘yan bindiga da ke cikin dazukan Birnin Magaji, Tsafe da Dansadau.
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi wani artabu mai zafi da wasu miyagun 'yan bindiga a jihar Zamfara.
Dakarun sojoji na rundunar Operation Fansan Yanma sun yi nasarar fatattakar 'yan bindiga bayan da suka kai musu hari a Zamfara.
Harin na na ’yan bindigan ya biyo bayan kisan da dakarun sojoji suka yi wa wani shahararren jagoran ’yan ta'adda mai suna Abu A.K tare da wasu daga cikin mabiyansa a wani artabu da suka yi a karammar hukumar Tsafe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

