Janye Biza: Wole Soyinka Ya Dura kan Trump, Ya Kira Shi Mai Mulkin Dan Kama Karya
- Farfesa Wole Soyinka ya ce shugaban Amurka Donald Trump yana da halayen kama-karya irin na tsohon shugaba Idi Amin
- Soyinka ya danganta janye masa biza da Amurka ta yi da tsauraran manufofin Donald Trump kan batun shige da fice
- Amurka dai ta fito ta bayyana cewa janye bizar Soyinka ta yi dai dai da dokar gwamnati, amma ba ta bayyana dalili ba
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Legas - Shahararren marubucin Najeriya kuma mai rike da lambar yabo ta Nobel, Farfesa Wole Soyinka, yi maganganu kan shugaban Amurka, Donald Trump.
Wole Soyinka ya bayyana Shugaban Amurka Donald Trump a matsayin “mai mulkin kama karya,” wanda ya yi kama da tsohon shugaban Uganda, Idi Amin.

Source: Facebook
Soyinka ya kira Trump 'dan kama karya'
Soyinka, mai shekaru 91, ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC Africa, kamar yadda kafar watsa labaran ta wallafa bidiyon a shafinta na Instagram.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin hirar, marubucin ya alakanta janye masa bizarsa ta shiga Amurka da irin tsauraran matakan da gwamnatin Trump ke ɗauka kan batun shige da fice.
“Wannan mutumin karamin mai mulkin kama-karya ne. Na taɓa faɗa tun kafin ya hau mulki cewa abu na farko da zai yi shi ne soke katin zama dan Amurka na dindindin.
"A lokacin na ce, ba zan jira a kore ni ba — zan tafi da kaina. Wannan shi ne abin da ya yake faruwa yanzu."
- Wole Soyinka.
Ya ƙara da cewa bayan Trump ya hau mulki, ya samu wasiƙa daga hukumar IRS (mai kula da haraji) tana umartarsa da ya je a binciki harajinsa, lamarin da ya kira “abin mamaki mai kama da ramuwar gayya.”
Soyinka ya kafa sharadin karbar bizar Amurka
Soyinka ya bayyana cewa ba shi da matsala da mutanen Amurka, amma ba zai sake zuwa ofishin jakadancin domin neman biza ba.
“Zan karɓi biza ne kawai idan gwamnati ta fahimci cewa an yi mun rashin adalci. Ba don na yi wani laifi ba, amma don tsattsauran ra’ayi irin na gwamnatin Trump."
- Wole Soyinka.
Ya tabbatar da cewa ofishin jakadancin Amurka a Legas ya aiko masa da wasiƙar janye biza ɗinsa ta B1/B2 a ranar 23 ga Oktoba, 2025, ba tare da bayyana takamaiman dalili ba.
Marubucin litattafan ya ce ba ya tunanin ya yi wani abu da ya saba dokar Amurka, kawai dai ya san wasu ƙananan al'amura sun faru shekaru da dama da suka wuce.

Source: Getty Images
Amurka ya yi bayani kan janye bizar Soyinka
A wani martani da jaridar The Punch ta samu daga ofishin jakadancin Amurka a Legas, jami’ar hulɗar jama’a, Julia McKay ta bayyana cewa biza ba hakki ba ne, gata ne da za a iya janye wa a kowane lokaci.
“Gwamnatin Amurka tana da ikon janye bizarta a duk lokacin da ta ga dama. Ba mu da izinin bayyana bayanan mutum saboda dokar sirri ta bizar,” in ji McKay.
Ta ƙara da cewa batun da ya shafi Wole Soyinka ba zai iya zama abin tattaunawa a bainar jama’a ba saboda dokokin tsaron bayanai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


