Mataimakin Kakakin Majalisar Kebbi Ya Aiko 'Sakon Murya' daga Hannun 'Yan Bindiga
- An fara yada wani sakon murya da ake zargin ya fito daga mataimakin kakakin Majalisar Dokokin jihar Kebbi, Hon. Sama'ila Muhammad Bagudu
- A makon jiya ne wasu yan bindiga sunnyi awon gaba da dan Majalisar yayin da suka shiga mahaifarsa watau Bagudu
- Rundunar yan sanda da sauran hukumomin tsaro a jihar kebbi ba su ce komai ba kan wannan sautin murya da ake yadawa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kebbi - Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, Hon. Sama’ila Muhammad Bagudu, wanda yan bindiga suka yi garkuwa da shi, ya aiko sakon murya.
A ranar Juma'a, 31 ga watan Oktoba, 2025 ne aka samu labarin wasu tsagerun yan bindiga sun sace dan majalisar a garin Bagudu a jihar Kebbi.

Source: Facebook
Leadership ta tattaro cewa a cikin wani sautin murya da ke yawo a kafafen sada zumunta a Birnin Kebbi, an ji murya mai kama da ta mataimakin kakakin majalisar yana magana kan kuɗin fansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane sako dan Majalisar ya aiko?
A sautin muryar, Hon. Sama’ila ya ba da sakon yadda za a tara kudin fansar da yan bindigan ke bukata domin sako shi.
A cewar sautin muryar, an riga an tara Naira miliyan 140, inda ya umarci ɗaya daga cikin abokan aikinsa a majalisar dokokin jihar Kebbi da ya sayar da motocinsa huɗu.
Ya amince a sayar da motocinsa ne domin hada kudin da masu garkuwa da shi suka nema.
Rahotanni da ba a tabbatar ba sun nuna cewa masu garkuwa da mataimakin kakakin majalisar sun nemi fiye da Naira miliyan 200 miliyan a matsayin kudin fansa kafin su sake shi.
Da gaske sautin muryar Hon. Sama'ila ne?
Sai dai a yayin da aka tuntubi ɗaya daga cikin abokai na kusa da Hon. Sama’ila Muhammad, Malam Abubakar Bagudo, ya ce bai tabbatar da ingancin sautin muryar ba.
Malam Abubakar ya ce:

Kara karanta wannan
'Yan majalisar Amurka sun taso Miyetti Allah a gaba kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
“Ba mu san daga ina wannan sauti ya fito ba, kuma ba mu tabbata cewa muryar da ke cikin sautin daga gare shi take kai tsaye ba.
"Mun yi mamakin jin irin wannan saƙo, domin Mataimakin Kakakin Majalisa mutum ne da ke da alaƙa ta kusa da mu, da yana da wani sako kamar haka, da ya sanar da mu kafin a ji shi a kafafen sada zumunta.”

Source: Facebook
Wasu rahotanni sun yi ikirarin cewa Mataimakin Kakakin Majalisar na ƙoƙarin tattara kuɗin da masu garkuwa suka nema domin a sako shi, watakila kafin ƙarshen makon nan.
Har yanzu jami’an tsaro a jihar Kebbi ba su fitar da wata sanarwa ba game da wannan lamarin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yadda aka sace 'dan majalisar Kebbi
A wani labarin, mun kawo muku cewa rundunar ‘yan sandan ta tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace mataimakin kakakin majalisar Kebbi, Hon. Sama'ila Muhammad.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar, ya ce an sace shi ne bayan ya kammala sallar Isha'i, yana shirin yafiya gida.
CSP Abubakar ya bayyana cewa rundunar ta dauki matakin gaggawa ta hanyar tura tawagar hadin gwiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda, sojoji, da 'yan sa-kai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

