Rikicin Manoma da Makiyaya: Mutane Sun Mutu a Harin Ramuwar Gayya a Benue
- Mutane sun rasa rayukansu yayin da aka kai harin ramuwar gayya a kauyen Anwule da ke karamar hukumar Ohimini a Benue
- Harin ya biyo bayan kisan wani makiyayi da ake zargin wasu mazauna kauyen suka aikata a ƙarshen watan Agustan 2025
- Mahukunta sun kai ziyara yankin, inda suka roƙi jama’a su kwantar da hankalinsu yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da bincike
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Benue - Mutane sun mutu yayin da ake neman mutum daya sakamakon wani harin ramuwar gayya da ake zargin wasu makiyaya sun kai Benue.
Rahotanni sun bayyana cewa an kai harin ne a kauyen Anwule da ke cikin karamar hukumar Ohimini.

Source: Facebook
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa harin ya faru ne a safiyar Talata, bayan wata matsala da ta samo asali daga kisan wani makiyayi matashi a ƙarshen watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Lamarin ya haifar da fargaba mai tsanani a yankin, inda ake ci gaba da tsoron karin rikici tsakanin manoma da makiyaya.
Tushen rikicin da aka yi a Benue
A cewar majiyoyin tsaro, matsalar ta fara ne a ƙarshen watan Agustan 2025 lokacin da wasu mazauna kauyen suka farmaki makiyayi, suka kashe shi bayan sun zarge shi da lalata gonakinsu.
An ce:
"Sun kai hari kan shanun, kuma a cikin rikicin ne saurayin da yake kiwon su ya mutu. Har yanzu ba a sami gawarsa ba,”
Bayan kisan, dangin makiyayin da abokan aikinsa suka shiga bincike don gano gawarsa, lamarin da ya kara tsananta fargaba tsakanin bangarorin biyu.
An kai harin ramakon gayya Benue
Rahotanni sun ce maimakon lamarin ya lafa, rikicin ya kara tashi bayan da wasu mazauna yankin suka sake kai hari ga wasu makiyaya a ranar Litinin, inda aka kashe makiyayi da raunata wasu.
Wannan ne ya zama abin da ya tayar da kura, inda aka sake samun harin ramuwar gayya a safiyar Talata.
Kafin dakarun soji daga sansanin Forward Operating Base da ke Otukpo su isa, makiyayan da ake zargi sun kutsa cikin kauyen Anwule, sun farmaki gidaje.
A ƙarshe, mutane uku — Simon Nbach, Adoya Ejigai, da Ejeh Loko — suka mutu, yayin da har yanzu ba a san inda mutum ɗaya yake ba.
Tasirin rikicin da matakin gwamnati
Dakarun soji daga baya sun taimaka wajen ciro gawarwakin waɗanda suka mutu, yayin da wasu mazauna yankin suka tsere zuwa kauyuka makwabta saboda tsoron wani harin.
A cikin martaninsu, hadimin gwamnan jihar kan tsaro, Joseph Har, tare da shugaban karamar hukumar Ohimini, Gabriel Adole, sun kai ziyara yankin don kwantar da hankalin jama’a.

Source: Facebook
Sun yi kira da a kwantar da hankali tare da tabbatar da cewa jami’an tsaro suna bin sawun wadanda suka aikata ta’addancin.
'Yan bindiga: Gwamnatin Kano ta yi zama
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi zama da shugabannin tsaro kan harin 'yan bindiga.
Abba Kabir ya zauna da sojoji, 'yan sanda da sauran masu ruwa da tsaki domin lalumo hanyar magance matsalar 'yan bindiga a jihar.
An yi zaman ne bayan wasu 'yan bindiga da ake zargi daga Katsina suka fito sun kai hari sun kashe mutane a karamar hukumar Shanono.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


