Gwamna Ya Fadawa Trump yadda Kiristoci ke Kashe Kiristoci a Kudancin Najeriya
- Gwamna Chukwuma Charles Soludo ya yi wa shugaban Amurka, Donald Trump martani kan zargin kisan Kiristoci a Najeriya
- Soludo ya bukaci a gabatar da hujjoji na yankan shakku kafin a yanke hukunci ko neman tsoma bakin kasashen waje
- Ya ce yawancin tashin hankali a Kudu maso Gabas ba na addini bane, inda hare-hare ke faruwa tsakanin Kiristocin yankin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Anambra — Gwamnan Jihar Anambra, Chukwuma Charles Soludo, ya bayyana cewa kalaman Shugaba Donald Trump game da turo dakarun Amurka zuwa Najeriya sun wuce gona da iri.
Gwamnan ya jaddada cewa matsalolin tsaro a Najeriya sun fi kama da rikicin cikin gida da siyasa fiye da rikicin addini.

Source: Twitter
The Cable ta rahoto cewa Soludo ya fadi haka ne a wata hira da ‘yan jarida a ranar Lahadi, inda ya bukaci a gabatar da cikakken bayanai da hujjoji.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi nuni da cewa duk wata kafa ta neman taimakon kasashen waje dole ne ta bi ka’idojin doka da mutunta ‘yancin kasashe.
Kiristoci na kashe Kiristoci inji Soludo
Gwamna Soludo ya ce a yankin Kudu maso Gabas, mafi yawancin wadanda suke buya a dazuka suna kashe mutane Kiristoci ne masu suna kamar Emmanuel, Peter, da John.
“Mutane suna kashe kawunansu — Kiristoci na kashe Kiristoci,”
Inji Soludo, yana mai jaddada cewa rikicin ba na addini ba ne.
A cewarsa, wannan ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga rikice-rikicen cikin gida, ‘yan bindiga, rikicin kabilanci da matsalolin tattalin arziki, ba yunkurin kishin addini ba.
Saboda haka, ya bukaci a yi amfani da tattaunawa ta kasa baki daya domin fahimtar musabbabin matsalolin da yadda za a warware su.
Me ya kamata Trump ya yi?
Soludo ya jaddada cewa duk wata bukata ta neman taimakon soja daga kasashen waje ya kamata ta zo ne ta hanyar neman izini daga gwamnatin tarayya, ba ta hanyar barazana ba.
Ya ce gwamnatocin kasashe za su iya neman tallafi ta hanyar hadin gwiwa kan fasaha, horo da kayan aiki, amma ba ta hanyar barazanar mamaya da take keta 'yancin kasashe ba.

Source: Twitter
Soludo ya bukaci a mayar da hankali kan tattaunawa a fadin kasa, hadin kai tsakanin shugabanni da kare ‘yancin Najeriya.
Tasirin kalaman wajen siyasa da zabe
Gwamnan ya kuma ambaci cewa yana sane da cewa kalamai irin wannan na iya shafar ra’ayin jama’a kafin zabe, kasancewarsa dan takara mai neman tazarce a makon gobe.
Duk da haka, TVC ta rahoto cewa gwamnan ya nuna muhimmancin bayyana gaskiya kan al’ummar yankin da kuma gujewa yin amfani da maganganu da za su raba jama’a.
Ya yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da daukar matakan tsaro tare da bude hanyoyin shari’a da tattaunawa domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.
Martanin Sowore da Donald Trump
A wani labarin, mun kawo muku cewa dan gwagwarmaya, Omoyele Sowore ya yi magana kan barazanar Amurka ta zuwa Najeriya.
Sowore ya ce wasu za su iya jin dadin hakan a farko, amma daga karshe ba za su yi farin ciki da hadarin da za a shiga ba.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya
Ya kawo misali da kasashe kamar Iraq, Libya da Syria da Amurka ta shiga da sunan kawo zaman lafiya amma aka samu karin matsaloli.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

