Steady Boy: NDLEA Ta Cafke Sanannen Mawaki, An Gano Dakin Hada Miyagun Kwayoyi

Steady Boy: NDLEA Ta Cafke Sanannen Mawaki, An Gano Dakin Hada Miyagun Kwayoyi

  • NDLEA ta kama matashin mawaki Steady Boy bayan gano kilo 77.2 na miyagun kwayoyi da aka shigo da su daga Amurka
  • Hukumar ta gano dakin hada miyagun kwayoyi a Ajao Estate, inda ake sarrafa “Colorado” da wasu sinadarai masu haɗari
  • Jami’an NDLEA sun kuma kama mutane da kwayoyi sama da kilo 200 a Lagos da Kaduna yayin samamen da suka gudanar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Hukumar NDLEA ta kama wani sanannen mawakin Najeriya, Godspower George Osahenrumwen, wanda aka fi sani da Steady Boy.

An kama Steady Boy bisa zargin karɓar kwayoyi daga Amurka a madadin wata kungiyar safarar miyagun kwayoyi da ke da alaka da manajansa, Zion Osazee Omigie (Zee Money).

Jami'an hukumar NDLEA sun kama mawakin Najeriya, Steady Boy bisa zargin karbar miyagun kwayoyi.
Jami'an hukumar NDLEA sun sauraron jawabi daga wani shugabansu. Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

Miyagun kwayoyi: NDLEA ta kama mawaki

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace masu ibada 20, sun hallaka malamin addini a Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta bayyana cewa an kama Steady Boy ne a gidansa da ke Bougain Villa, Primewater Gardens 2, Freedom Way, Lekki, jihar Legas.

Hakan ta faru ne bayan an gano kilo 77.20 na miyagun kwayoyi nau’in 'Loud; da aka ɓoye cikin akwatunan kayan masai da aka shigo da su daga Amurka ta hanyar jirgin DHL a ranar Talata.

“Steady Boy ya bayyana kansa a matsayin wanda zai karɓi wadannan miyagun kwayoyi a madadin wata kungiyar safarar kwayoyi da ke da reshe a kasashen waje,” in ji Babafemi.

Ya kara da cewa, bincike ya nuna manajan mawakin, Zee Money, shi ne ke jagorantar safarar kwayoyin, amma ya tsere bayan kama Steady Boy.

An gano dakin hada miyagun kwayoyi

Bayan watanni na leƙen asiri, NDLEA ce jami'anta sun kuma gano dakin hada kwayoyi a Ajao Estate, Lagos, inda ake samar da Colorado da wasu kwayoyi masu haɗari.

Kara karanta wannan

Gwamna Dauda ya fadi matsalar sulhu da 'yan bindiga, ya yi gargadi

An kwato sababbin kwayoyi nau’in Colos masu nauyin kilo 16.2, ADB-CHMNACA kilo 1.7, Potassium Carbonate kilo 4.5, da lita 91 na sinadarin Dibromobutane.

Haka zalika, sanarwar ta bayyana cewa jami'an NDLEA sun kama wanda ake zargi da mallakar dakin hada miyagun kwayoyin tare da kayan hada kwayoyin.

Hukumar NDLEA ta tsaurara yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi.
Shugaban hukumar NDLEA na kasa, Mohammed Buba Marwa. Hoto: @ndlea_nigeria
Source: Twitter

NDLEA ta tsaurara yaki da miyagun kwayoyi

A wani samame a Mushin da ke Legas, jami’an NDLEA sun kama Afeez Salisu (28), wanda aka fi sani da Malu, inda aka samu kilo 16.4 na “Ghana Loud” da kwalabe da sachet na Colorado.

A Kaduna, an kama kwayoyi 84,710 na Tramadol da ake safararsu daga Onitsha zuwa Bauchi, inda daga baya aka kama mai karɓar kayan, Musa Abdulkarim (27).

Haka kuma, an kama Hamza Musa (47) da kwalaben Akuskura 32,946 a hanyar Abuja–Kaduna, da Saidu Nafiu (30) da kilo 131.5 na skunk a karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Babafemi ya jaddada cewa NDLEA ba za ta sassauta ba wajen murkushe masu safarar kwayoyi, tare da tabbatar da cewa duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Kara karanta wannan

Masu safarar kwayoyi sun bude wuta kan jami'an NDLEA da sojoji

Masu safarar kwayoyi sun harbi jami'an NDLEA

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) da sojoji sun fuskaci hari a jihar Edo.

Jami'an na NDLEA da sojojin sun fuskanci harin ne daga wajen masu fataucin kwayoyi a kauyen Ukpuje, karamar hukumar Owan ta Yamma ta jihar Edo.

Kwamandan NDLEA na Edo, Mitchel Ofeyeju ya ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga Oktoban 2025 yayin wani samamen hadin gwiwa domin lalata gonakin wiwi a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com