Jihohin da za su Jikkata idan Amurka ta Farmaki Najeriya da Sunan Yaki

Jihohin da za su Jikkata idan Amurka ta Farmaki Najeriya da Sunan Yaki

  • Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar kai wa Najeriya harin soja bayan ya zargi kasar da yin shuru ana kashe Kiristoci
  • Gwamnatin Najeriya ta karyata wannan zargi yayin da ‘yan kasa ke ci gaba da tattauna lamarin a kafafen sada zumunta
  • Legit.ng ta kawo jerin jihohin da ka iya fuskantar matsaloli idan Amurka ta aiwatar da wannan barazana

Washington, Amurka – Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, yana sanar da cewa ya umurci Ma’aikatar Yaƙin Amurka ta shirya daukar matakin soja kan Najeriya saboda “kisan Kiristoci” da ake zargi ana yi.

Sakataren tsaron Amurka, Pete Hegseth, wanda yake daidai da ministan tsaro a Najeriya, ya kara da cewa Amurka za ta dakatar da tallafinta ga Najeriya tare da tura sojoji don “rushe dukkan ‘yan ta’addan da ke yankin.”

A baya, shugaban Amurka ya saka Najeriya cikin jerin kasashen zaman Dardar lura da su a matsayin kasar da ke da matsanancin damuwan tsaro.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Amurka mai sukan Najeriya kan tsaro ya sassauto, ya yaba wa Tinubu

Jihohin da za su sha wahala idan Amurka ta farmaki Najeriya
Jihohin Arewa ne za su wahala idan Amurka ta farmaki Najeriya | Hoto: @PeterObi, @OpenEyeComms
Source: Twitter

Ko da yake ba a yi hasashen cewa Amurka za ta shiga yakin kai tsaye da Najeriya ba, kuma rundunar sojin Najeriya ba ta cikin tsare-tsaren farko idan har Amurka ta kai hare-hare kan ‘yan ta’adda, kalaman da suka fito daga Washington sun tayar da hankula a kasar.

A yayin da damuwar ke karuwa, Legit.ng ta yi nazari kan jihohin Najeriya da ka iya fuskantar matsalar harin soja idan Amurka ta dauki mataki.

1. Jihar Borno

Borno ita ce cibiyar ta’addanci a Najeriya. Tun shekaru da dama take fama da ta’addancin Boko Haram da kuma kungiyar ISWAP mai alaƙa da ISIS.

2. Jihar Yobe

Yobe tana daya daga cikin jihohin da ta’addanci ya fi shafa a Najeriya. An yi asarar rayuka masu yawa, mutane sun gudu daga gidajensu, kuma gine-gine da tattalin arziki sun lalace sakamakon hare-hare na Boko Haram da ISWAP.

3. Jihar Adamawa

Adamawa tana daga cikin jihohin da suka fi shan wahala daga hare-haren ‘yan ta’adda. Ana ci gaba da gudanar da ayyukan soja a yankin domin fatattakar mayakan ta’addanci.

Kara karanta wannan

'Kisan Kiristoci': Tawagar Amurka ta shigo Najeriya, ta yi magana da Ribadu

4. Jihar Kaduna

Matsalar tsaro a Kaduna ta zama wani bangare na rikicin da ke yawaita a Arewacin Najeriya. A watan Satumba, Gwamna Uba Sani ya gargadi ‘yan adawa da su daina siyasantar da batun tsaro, inda ya ce ikirarin cewa za a iya “tarwatsa ‘yan bindiga da bom” ba gaskiya ba ne.

Ya danganta matsalar tsaro da talauci, rashin aikin yi, da kuma gazawar shugabanci a matakai daban-daban.

5. Jihar Katsina

Katsina tana fama da hare-hare daga ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda. Sace mutane da kai hare-hare sun zama ruwan dare a jihar.

Gwamnan Kaduna kan batun tsaro
Gwamnan Kaduna, Uba Sani | Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

6. Jihar Zamfara

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin sa na shirin kafa ‘yan sandan jiha domin magance matsalolin tsaro a Zamfara da sauran jihohi.

Gwamna Dauda Lawal ya ce da zarar gwamnati ta samu cikakken iko kan harkar tsaro, matsalar ‘yan bindiga za ta zama tarihi.

7. Jihar Sokoto

Sokoto tana fama da matsalar ‘yan bindiga da satar mutane musamman a yankunan karkara da kan iyaka.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta dauki matakai 3 bayan sojoji sun yi yunkurin juyin mulki a Benin

A watan Satumba, rundunar ‘yan sandan Sokoto ta kama wasu mutum uku da ake zargi da taimaka wa ‘yan bindiga tare da kwato makamai da harsasai.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Ahmad Rufai, ya bayyana cewa an kama su ne a wani samame da aka yi bisa bayanan sirri.

8. Jihar Neja

Neja na daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da ta’addanci. Tazarar jihar da babban birnin tarayya (Abuja) na kusan kilomita 30 ne kawai, abin da ke nuna yadda barazanar ta yadu zuwa yankin tsakiyar kasar.

Sauran jihohin da ka iya shan tasiri idan Amurka ta kai hari:

  1. Kano
  2. Kogi
  3. Benue
  4. Filato
  5. Taraba
  6. Gombe
  7. Bauchi

Yakin da Najeriya ta yi a baya

A tun farko, shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, cewa ya umurci Ma’aikatar Yaƙi ta ƙasarsa da ta fara shirin daukar mataki kan Najeriya saboda “kisan Kiristoci.”

Trump ya ce, nan take za a dakatar da duk wani tallafi da taimako ko wata gudunmawa da Amurka ke bai wa Najeriya saboda zargin yiwa Kiristoci kisan gilla.

Kara karanta wannan

Najeriya ta janye jirgin yakinta zuwa Benin bayan sanin halin da ake ciki

Hakazalika, ya ce sojojin Amurka na iya shiga ƙasar da “makamai da ƙarfin tsiya” domin su “kawarda 'yan ta’addan Musulmai da ke aikata waɗannan mummunan laifuka.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng