Yadda Ta Kaya Tsakanin Buhari da Trump a White House kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya
- Tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari, ya taba ganawa da Shugaba Donald Trump na Amurka a fadar White House
- A yayin ganawar ta su, Shugaba Donald Trump ya tambayi Buhari dalilin da ya sa ake kashe Kiristoci a Najeriya
- Sai dai, a lokacin marigayi Buhari ya yi gamsashshen bayanin cewa abin da yake zargi ko kadan ba haka yake ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Abuja, Najeriya - Shekara guda kafin karshen wa’adin farko na tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya gana da Donald Trump.
Shugabannin guda biyu sun yi ganawar ne a fadar White House da ke Amurka.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa yayin ganawar Trump ya yi batun zargin kisan Kiristoci a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Trump ya tambaya ga Buhari kan Kiristoci
A lokacin, Trump, wanda shi ma yana wa’adin farko ne, ya kalli Buhari cikin ido da ido ya tambaye shi kai tsaye da cewa:

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya
“Me yasa kuke kashe Kiristoci a Najeriya?”
Buhari, wanda tambayar ta zo masa a bazata, ya tsaya da nutsuwa, bai nuna damuwa ba, ya bar Trump ya gama bayani kafin ya ba shi amsa a natse.
Wane martani Buhari ya yi wa Trump
Ya bayyana cewa rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya a Najeriya ba rikicin addini ba ne, amma na al’ada da muhalli, wanda ya samo asali ne daga karuwar jama’a da kuma sauyin yanayi.
Ya kuma danganta yaduwar makamai da rikice-rikicen da suka biyo bayan rushewar gwamnatin Libiya, abin da gwamnatin Amurka kanta ta amince da cewa an yi kuskure a lokacin gwamnatin Barack Obama.
“Mun yaba da goyon bayan da Amurka take ba mu a yakin da muke yi da ta’addanci, kuma mun nuna godiya bisa yarda da ta bayar wajen sayar mana da jiragen yaki na Super Tucano A-29 guda 12 da makamai domin inganta yaki da ta’addanci."
- Muhammadu Buhari
Buhari ya tuna ganawarsa da Trump
Shekara guda bayan fara wa’adinsa na biyu, Buhari ya sake tuna wannan ganawar yayin wani taron bita a Aso Rock.
“Lokacin da na gana da Trump a ofishinsa, mu biyu ne kawai. Ya kalle ni cikin ido ya ce, ‘Me yasa kuke kashe Kiristoci?’ Na yi mamaki, amma na daure, na kwantar da hankali na kuma gaya masa gaskiya cewa rikicin da ke tsakanin makiyaya da manoma ya dade da wanzuwa kafin ni, balle shi."
- Muhammadu Buhari
Tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa rikicin yana da nasaba da tsarin kiwo na gargajiya, karuwar jama’a, da tasirin sauyin yanayi, ba tare da wata alaka da addini ba.

Source: Facebook
“Saboda sauyin yanayi da karuwar jama’a, makiyaya suna bin hanyoyin ruwa da kiwo ba tare da la’akari da gonakin mutane ba. Matsalar ta al’ada ce, ba ta addini ba."
- Muhammadu Buhari
Buhari ya kuma shaida wa Trump cewa gwamnatocin da suka gabata sun kafa hanyoyin kiwo, da wuraren kiwo domin guje wa rikice-rikice, amma daga baya aka bar mutane suka mamaye hanyoyin, abin da ya ta’azzara matsalar.

Kara karanta wannan
Tinubu ya maida martani ga Shugaban Amurka, Trump kan zargin kisan kiristoci a Najeriya
Tsohon shugaban ya ce bayan bayanin da ya yi, Trump ya fahimci cewa rikicin da ke kasar ba na addini ba ne, amma na tarihi da al’ada.
“Ina tsammanin ni ne kaɗai shugaba a Afirka daga cikin kasashe masu tasowa da aka gayyata. Na yi kokarin na bayyana masa cewa rikicin da ke Najeriya yana da tushe na tarihi, ba na addini ba."
- Muhammadu Buhari
Tinubu zai gana da Trump
A wani labarin kuma, kun ji cewa fadar shugaban kasa ta bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai gana da Donald Trump.
Hadimin Tinubu ya bayyana cewa za a yi ganawar ne biy bayan zargin kisan Kiristoci a Najeriya da Trump ya yi.
Daniel Bwala ya ce shugabannin biyu za su gana ne a fadar Aso Rock ko White House nan bada jimawa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng