Ba na fatan sake ganawa da mutum kamar Buhari — Trump
- Shugaban Amurka ya bayyana Shugaba Buhari a matsayin mutum mara kuzari
- Majiyoyi sun nuna cewa Trum yace baya burin sake haduwa da Buhari
- Zuwa yanzu fadar shugaban kasa Buhari bata ce komai akan lamarin ba
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bayyanawa mataimakansa cewa ba ya burin sake ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari saboda "tamkar gawa" yake, shafin BBC Hausa ta ruwaito.
A watan Afrilu ne shugabannin biyu suka gana a fadar White House, ziyarar da a wancan lokacin mai magana da yawun Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya bayyana a matsayin amincewar da gwamnatin Trump ta yi wa gwamnatin Najeriya.

Sai dai jaridar Financial Times ta Burtaniya ta ambato wasu majiyoyi uku da ba sa son a fadi sunansu suna cewa Trump ya shaida musu cewa "har abada ba ya son sake ganawa da Shugaba Buhari saboda tamkar gawa" yake ba shi da kuzari.
Kawo yanzu fadar shugaban Najeriya ba ta mayar da martani ba kan batun duk da cewa Trump ya jinjina wa Buhari a bainal jama'a a yayin taron manema labarai da suka gudanar tare a wancan lokacin a Washington.
KU KARANTA KUMA: 2019: Daga Buhari har Oshiomhole ba zasu iya ceton Sani da sauransu ba - APC
Wannan na zuwa ne a yayin da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ke shirin ganawa da Trump a yau Litinin a fadar White House, yayin da jaridar ta Financial Times ta kara da cewa, ana fatan ganawarsu ta yau ta farfado da dangantaka tsakanin Amurka da yankin Afrika.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng