Najeriya Za ta Iya Karawa da Amurka? Tarihin Yaki 3 da Najeriya ta yi da Wasu Kasashe

Najeriya Za ta Iya Karawa da Amurka? Tarihin Yaki 3 da Najeriya ta yi da Wasu Kasashe

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya kira Najeriya "ƙasar da ta zubar da mutuncinta" kan wasu dalilai
  • Ya ce Amurka na iya shiga Najeriya domin kawar da 'yan ta’adda masu tsattsauran ra’ayin rikau na addinin Musulmai da ke kashe Kiristoci a kasar
  • Legit.ng ta duba tarihin yaƙe-yaƙe da rikice-rikicen soja da Najeriya ta taɓa shiga a shekarun baya un samun ‘yancin kai

Washington DC, Amurka – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, cewa ya umurci Ma’aikatar Yaƙi ta ƙasarsa da ta fara shirin daukar mataki kan Najeriya saboda “kisan Kiristoci.”

Trump ya ce, nan take za a dakatar da duk wani tallafi da taimako ko wata gudunmawa da Amurka ke bai wa Najeriya saboda zargin yiwa Kiristoci kisan gilla.

Hakazalika, y ace sojojin Amurka na iya shiga ƙasar da “makamai da ƙarfin tsiya” domin su “kawarda 'yan ta’addan Musulmai da ke aikata waɗannan mummunan laifuka.”

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Malamin addini ya 'gano' shirin Amurka kan gwamnatin Tinubu

A baya, Amurka ta sanya Najeriya cikin kasashen da ta ce akwai barazanar tsaro da zaman mutane, musamman ma’aikatan diflomasiyya.

Yakin Najeriya a kasashen waje
Shugaba Tinubu da mukarraban sojojinsa | Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, kasashen Afrika a zahiri ba lallai su iya shiga yaki da Amurka ba, kuma Amurka bata bayyana shiga yaki da Najeriya kai tsaye ba.

Sai dai, shin Najeriya ta taba shiga wani yaki da wasu kasashen waje? Legit.ng ta tattaro maku lokutan da Najeriya ta shiga yaki a tarihin kasar tun samun ‘yancin kai.

1. Yaƙin Najeriya da Biafra (1967–1970)

An fara Yaƙin Basasar Najeriya ranar 6 ga Yuli, 1967, aka kuma kammala a ranar 15 ga Janairu, 1970. Wannan rikici da aka fi sani da Biafran War ko Yaƙin Biafra, ya faru ne tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Biafra wadda ta balle daga ƙasar a 1967.

Dalilan yaƙin sun samo asali ne daga rikice-rikicen siyasa, ƙabilanci, al’adu da addini tun kafin Birtaniya ta kammala ba wa Najeriya ‘yancin kai daga 1960 zuwa 1963.

Babban abin da ya tayar da rikicin a 1966 sun haɗa da maimatuwar juyin mulki, da kuma kisan jama’ar kabilar Igbo a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci

2. Rikicin Najeriya da Kamaru kan yankin Bakassi (1980s–2000s)

Rikicin siyasa, ƙararraki da kuma musayar wuta lokaci-lokaci sun jinkirta mika yankin Bakassi daga Najeriya zuwa Kamaru.

Ko da yake an samu rashin jituwa ta diflomasiyya, ba a kai ga cikakken yaƙi ba tsakanin Najeriya da Kamuru ba.

A shekarar 2008, Najeriya ta kammala mika yankin Bakassi ga Kamaru bayan hukuncin Kotun Duniya (ICJ) a 2002 wanda ya bai wa Kamaru wannan yankin.

Lokacin da aka yi yakin Biafra
Wadanda ke kan gaba a yakin Biafra | Hoto: @Pirtim
Source: Twitter

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjejeniyar Green Tree Agreement a 2006 domin tabbatar da mika yankin cikin lumana, abin da ya kammala a ranar 14 ga Agusta, 2008 duk da cece-kuce da adawa daga ‘yan Najeriya da dama.

3. Yaƙin Liberia da Sierra Leone (1990s–2000)

Ta hannun rundunar tsaron ƙasashen Yammacin Afirka (ECOMOG) da ƙungiyar ECOWAS ta kafa, Najeriya ta jagoranci yaƙin tsoma baki a kasashen Sierra Leone da Liberia.

A lokacin mulkin Olusegun Obasanjo, Najeriya ce ta fi ɗaukar nauyin rundunar ECOMOG wadda ta kai sojoji har 15,000 a Liberia, sannan ta yi aiki a makwabciyar ƙasa, Sierra Leone, kamar yadda The New Humanitarian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a Najeriya

Wadannan su ne yakoki da Najeriya ta shiga da wasu kasashen duniya a baya, kuma a halin yanzu, akwai batutuwa da dama da ke tattare da yankin Biafra da su Nnamdi Kanu ke fafutukar kafawa.

Yunkurin kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa

A bangare guda, an kara samun ‘yan aware daga yankin Yarbawa a Najeriya, inda mutane irinsu Sunday Igboho ke kokarin ganin sun balled aga Najeriya.

Duk da an samu kiraye-kiraye daga ‘yan siyasar yankin kan makomar kafa kasar, ya zuwa yanzu babu wani karfi da tafiyar ta yi kamar dai yadda Biafra ya kasance.

Sai dai, akwai masu ganin a iya amfani da siyasa wajen ganin yankin Yarbawa ya balle daga Najeriya kamar yadda masu fafutukar ke bukata.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng