Lauya a Amurka Ya Saba da Trump kan Barazana ga Najeriya, Ya Fadi Ciwon da Ke Damunsa

Lauya a Amurka Ya Saba da Trump kan Barazana ga Najeriya, Ya Fadi Ciwon da Ke Damunsa

  • Shugaba Donald Trump ya sake tayar da kura kan Najeriya bayan barazanar matakin soji a kasar
  • Sai dai babban lauya a Amurka, Ron Filipkowski ya ce maganganunsa kan yi kama da rashin daidaituwar hankali
  • Filipkowski ya yi martani bayan Trump ya lissafa yiwuwar kai farmaki a Najeriya, yana zargin gwamnati da kasa kare Kiristoci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, US - Wani lauya kuma tsohon mai gabatar da kara na Amurka, Ron Filipkowski ya soki Donald Trump kan barazana ga Najeriya.

Filipkowski ya yi zargin cewa Shugaba Donald Trump na iya samun matsalar kwakwalwa saboda kalamansa kan Najeriya kan zargin kisan Kiristoci.

Lauya a Amurka ya taso Trump a gaba kan barazana ga Najeriya
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump. Hoto: Getty Images.
Source: Getty Images

Hakan na cikin wani rubutu da Filipkowski ya yi a shafinsa na X a yau Lahadi 2 ga watan Nuwambar 2025 inda ya soki tunanin shugaba Trump.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi martani bayan Trump ya yi barazanar kawo hari a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zargin kisan Kiristoci: Barazanar Trump ga Najeriya

Filipkowski ya yi wannan tsokaci bayan Trump ya umurci Ma’aikatar Yaki ta Amurka ta fara shiri na yiwuwar daukar matakin soja kan Najeriya saboda kare Kiristoci.

Trump ya ce Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi ga Najeriya idan kisan Kiristoci bai tsaya ba, kuma tana iya shiga kasar da karfi sosai.

Ya kara cewa duk wani farmaki zai kasance cikin gaggawa, tsauri, da tsabta, yana gargadin gwamnatin Najeriya ta dauki mataki cikin gaggawa don kare Kiristoci.

Trump ya tabbar cewa Amurka ba za ta tsaya ta kalli Kiristoci a Najeriya da sauran wurare suna fuskantar hari ba, tana shirye ta kare su.

Babban lauya a Amurka ya caccaki Trump

Sai dai Filipkowski duk da kasancewarsa dan Amurka ya caccaki kalaman Trump kan Najeriya.

Filipkowski ya ce abin takaici ne yadda shugaban ke furta irin wadannan kalamai da suka yi kama na rashin tunani.

Kara karanta wannan

Barazanar Trump: Malamin addini ya 'gano' shirin Amurka kan gwamnatin Tinubu

Ya ce a yanzu za a iya daukar maganar Trump a matsayin na rashin hankali da kuma hangen nesa.

Ya ce:

"A wasu lokutan, za mu iya daukar kalamansa ko kuma shi kansa a matsayin mai tabin ƙwaƙwalwa."

Martanin mutane kan abin da lauyan ya ce

Mutane masu ta'ammali da kafar sadarwa sun yi martani daban-daban kan abin da babban lauyan ya rubuta bayan barazana da Trump ya yi ga Najeriya.

@terri4436:

"Duk lokacin da Trump ya yi barazana ga wani, to akwai abin da yake harin samu musamman ma'adinai.
" Zinare na daya daga cikin ma'adinai masu daraja a Najeriya, sannan akwai wasu da dama da ake samu duk da karancin da suke da shi. "

@wedietz:

"Yana tunanin zuwa Najeriya ya kawo karshen wadannan yan ta'addan zai zama da sauki? Shin ba mu koyi wani abu ba a baya."

Fasto ya fadi shirin Trump kan gwamnatin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya ya gargadi Shugaba Bola Tinubu game da barazanar Amurka a kasar.

Kara karanta wannan

Hana shari'ar Musulunci a Najeriya: Bashir Ahmad ya yi martani mai zafi kan sanatan Amurka

Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Tinubu kan zargin kisan Kiristoci da Amurka ke ta yadawa, yana cewa akwai shirin kawar da gwamnati.

Ayodele ya ce ya dade yana gargaɗi game da hatsarin Amurka ga gwamnatin Tinubu inda ya ce suna shirya manakisa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.