Barazanar Trump: Malamin Addini Ya 'Gano' Shirin Amurka kan Gwamnatin Tinubu

Barazanar Trump: Malamin Addini Ya 'Gano' Shirin Amurka kan Gwamnatin Tinubu

  • Fitaccen malamin addinin Kirista a Najeriya ya gargadi Shugaba Bola Tinubu game da barazanar Amurka a kasar
  • Fasto Elijah Ayodele ya gargadi Tinubu kan zargin kisan Kiristoci da Amurka ke ta yadawa, yana cewa akwai shirin kawar da gwamnati
  • Ayodele ya ce ya dade yana gargaɗi game da hatsarin Amurka ga gwamnatin Tinubu inda ya ce suna shirya manakisa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Ayodele, ya yi magana kan barazanar Amurka.

Ayodele ya gargadi Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kasance cikin shiri kan zargin kisan Kiristoci da Amurka ke ta yadawa.

Ana zargin Amurka da neman kifar da gwamnatin Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Donald Trump na Amurka. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Donald Trump.
Source: Facebook

A wata sanarwa da mai taimaka masa Osho Oluwatosin ya fitar, Ayodele ya ce ya dade yana magana kan shirin Amurka game da gwamnatin Tinubu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Amurka ta gindayawa Najeriya sharadi bayan barazanar kawo hari kan zargin kisan kiristoci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barazanar da Trump ya yi wa Najeriya

A jiya ne Shugaban Amurka, Donald Trump ya yi barazanar aika sojojin Amurka zuwa Najeriya idan gwamnati ta gaza daukar matakai.

Hakan na zuwa bayan Amurka ta nuna damuwa kan zargin yiwa Kiristoci kisan kiyashi wanda ya tayar da hankula.

Trump ya ce zai hana Najeriya tallafin ketare, ya kuma dauki mataki “mai tsauri cikin gaggawa” kan masu tayar da kayar baya.

Gwamnatin Amurka ta zargi Najeriya da “kisan Kiristoci”, inda Shugaba Donald Trump ya yi barazanar jan layi kan kasar.

Trump: Fasto Ayodele ya gargadi Tinubu

Ayodele ya ce wannan duk shirin adawa ne da ake yi don a kawar da Tinubu daga mulki kafin 2027 ko kuma a lokacin zaɓe.

Ya ce:

“Ina ta cewa Amurka na fafatawa da gwamnatin Tinubu, amma ba a kula ba. Na faɗi batun juyin mulki, suka ce ba zai faru ba.

Kara karanta wannan

Zargin kisan Kiristoci: Trump ya yi barazanar daukar matakin soji a Najeriya

“Wasu na kirana Faston hasashe ko na bala'i, amma abubuwan da nake faɗi suna bayyana a fili."
Malami ya gargadi Tinubu game da Amurka
Fasto Elijah Ayodele da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Primate Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

An zargi Amurka da shirin kifar da Tinubu

Ayodele ya ce gwamnatin Tinubu ka da ta yi sakaci, wannan shiri ne na hambarar da gwamnati a 2027, ba kawai zargi ba.

Ya yi gargadin cewa shirin na nufin raunana gwamnatin Tinubu domin adawa ta samu damar karfi ta koma kan mulki.

Ya bayyana cewa wasu manyan kasashen duniya sun gama shirye-shiryensu da wasu ‘yan adawa a Najeriya domin su kawar da Tinubu daga ofis.

“Kai Tinubu, ko ka so ko baka so, wannan alama ce. Kar ka yi barci, akwai matsala. Ka nemi taimakon Allah."

- Elijah Ayodele

Ya ce gwamnatin Amurka “ba ta son Tinubu a 2027” saboda wannan rikici da ake ta yadawa kan Kiristoci.

Zargin kisan Kiristoci: Ndume ya zargi majalisa

Kun ki cewa Sanata Ali Ndume ya ce sakacin Gwamnati da Majalisa ne suka jawo saka Najeriya a jerin kasashen da ke da matsalar 'yancin addini.

Kara karanta wannan

Kisan kiristoci: Sanata Ndume ya dora laifi kan gwamnatin Tinubu da Majalisar Dattawa

A ranar Juma'a 31 ga watan Oktobar 2025, Shugaba Donald Trump na Amurka ya maida sunan Najeriya cikin jerin wadannan kasashe saboda zargin kisan kiristoci.

Ali Ndume ya ce tun farko ya hango wannan matsalar kuma ya ankarar da gwamnatin Bola Tinubu da Majalisa amma suka yi biris.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.