Kano: ’Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane bayan Sace da Dama, an 'Gano' inda Suka Fito
- Fargaba ta karade wasu kananan hukumomi a Kano bayan hare-haren ‘yan bindiga da suka kashe mutane uku tare da yin garkuwa cikin mako guda
- Shugabannin yankin sun ce maharan na shigowa daga Katsina ta hanyoyin daji, suna kai farmaki duk da kasancewar dakarun tsaro a yankin
- Shugabannin yankin sun roki Shugaban Najeriya Bola Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf su dauki matakin gaggawa kan lamarin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - An samu tashin hankali a wasu kananan hukumomi na jihar Kano bayan jerin hare-haren ‘yan bindiga da ake zargin sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu.
Rahotanni sun nuna cewa Shanono, Bagwai da Tsanyawa na cikin yankunan da ake ta kai hare-hare duk da zuwan jami’an tsaro masu makamai a wuraren.

Source: Facebook
Yadda yan bindiga suka addabi yankunan Kano
Da yake zantawa da manema labarai a Kano, Hakimin Faruruwa, Mustapha Abubakar ya ce lamarin na kara tsananta kuma jama’a na cikin tsoro, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa:
“A cikin kwana uku da suka gabata, mutane da dama sun rasa rayukansu, an kuma sace matasa maza da mata a yankinmu.”
A cewarsa, ‘yan bindigan kan shigo daga jihar Katsina ta hanyoyin daji, inda ake zargin suna samun kariya daga wasu al’ummomi a can.
Ya ci gaba da cewa:
“Yan bindiga na shigo ta hanyoyin da suka hada Katsina da kauyukanmu, suna kaucewa wuraren jami’an tsaro ba tare da katsewa ba.”

Source: Original
Rokon da aka yiwa Tinubu, Abba Kabir
Hakimin ya yi kira ga dakarun sojoji su canja dabaru ta hanyar mamaye dukkan hanyoyin daji da maharan ke bi domin kauce musu.
Shi ma shugaban kwamitin tsaron Faruruwa, Alhaji Yahya Bagobiri, ya koka cewa hare-haren sun karu, lamarin da ya jefa mutane cikin matsanancin fargaba.
“In kasa da mako guda, an sace mutane da dama, jiya ma mutum daya an yanka shi a gidansa aka tafi da ‘ya’yansa."

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki
- Alhaji Yahya Bagobiri
Ya ce wasu sun bar gidajensu, wasu kuma ba sa komawa ganin iyalansu saboda tsoron farmakin ‘yan bindiga a kowane lokaci, kamar yadda Vanguard ta ce.
Bagobiri ya roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf su dauki matakin gaggawa don hana maharan mamaye yankin gaba daya.
Ya ce:
“Abin da wadannan barayi ke kokarin yi shi ne su mamaye Shanono, Tsanyawa, Bagwai, Gwarzo da Bichi sannan su kewaye Kano.”
Kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda bai yi nasara ba, amma majiya ta ce har yanzu ba a samu rahoton kai tsaye daga yankunan ba.
Yanzu haka, jama’ar yankin na rayuwa cikin tsananin fargaba tare da kira ga hukumomi su dauki matakan gaggawa domin dawo da tsaro da kwanciyar hankali.
Yan bindiga sun kai hari a Kano
Mun ba ku labarin cewa an shiga jimami bayan 'yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Kano.
Miyagun 'yan bindigan sun kai farmakin ne a karamar hukumar Shanono inda suka yi kisa tare da sace dabbobi masu yawa.
Majiyoyi sun bayyana 'yan bindigan sun zo a kan babura inda suka rika harbi domin firgita mutane kafin daga bisani su kwashe kayayyaki.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

