An Yi Babban Rashi: Mahaifiyar Tsohon Gwamna, Adamu Mu’azu Ta Bar Duniya

An Yi Babban Rashi: Mahaifiyar Tsohon Gwamna, Adamu Mu’azu Ta Bar Duniya

  • Tsohon gwamnan Bauchi, Ahmad Adamu Mu’azu, ya yi rashin mahaifiyarsa bayan ta sha fama da jinya inda al'umma suka yi mata addu'o'i
  • Gwamna Bala Mohammed ya bayyana jimaminsa, yana cewa marigayiyar ta yi rayuwa ta ibada, zumunci da son jama’a
  • Gwamnan ya mika ta’aziyya ga iyalan Adamu Mu’azu, yana addu’ar Allah ya gafarta mata ya kai ta Aljanna Firdausi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Bauchi - Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi ya yi rashin mahaifiyarsa .

Majiyoyi sun ce Ahmad Adamu Mu'azu ya rasa mahaifiyarsa ne a yau Asabar 1 ga watan Nuwambar 2025 bayan fama da jinya.

Gwamna Bala ya jajantawa Adamu Mu'azu kan rashin mahaifiya
Tsohon gwamna Adamu Mu'azu da Gwamna Bala Mohammed. Hoto: Senator Bala Abdukadir Mohammed.
Source: Facebook

Ta'aziyyar Gwamna Bala ga Adamu Mu'azu

Hakan na cikin wata sanarwa da Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya fitar a shafinsa na Facebook a yammacin yau Asabar 1 ga watan Nuwambar 2025.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP ya dauki sabon salo, an dakatar da manyan shugabannin jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar da cewa marigayiyar ta sha fama da jinya kafin ta ce ga garinku wanda ya jawo hankalin al'umma tare da yi mata addu'o'i.

Gwamna Bala Mohammed ya nuna alhininsa game da rasuwar dattijuwar inda ya ce tabbas an yi babban rashi a jihar da Najeriya baki daya.

Sanarwar ta ce:

Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun....
Cikin alhini tare da fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki, muka wayi gari da rasuwar ɗaya daga cikin iyayen mu mata da suka rage, mahaifiyar tsohon gwamnan jihar Bauchi, Alhaji (Dr) Ahmed Adamu Muazu ( Walin Bauchi), bayan fama da jinya."
Gwamna Bala ya fadi halayen marigayi mahaifiyar Adamu Mu'azu
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi. Hoto: Senator Bala Abdulkadir Mohammed.
Source: Twitter

Gwamnan ya bayyana halayen marigayiyyar na kirki da suka hada da bautar Allah da zikiri, sada zumunci da kuma nuna halin son jama'a.

Bala Mohammed ya tura sakon ta'aziyya a madadin daukacin al'ummar Bauchi, gwamnatin jihar da iyalansa bisa rashin da babban yayansa, Wali ya yi.

Daga karshe, ya yi addu'ar Allah ya yi mata rahama kuma ya sanya ta gidan aljannar Firdausi madaukakiya.

Kara karanta wannan

Nuhu Ribadu da Birtaniya sun yi alhini da kwamishinan tsaro ya rasu a hadarin mota

"Rasuwar Hajiya ta haifar da wagegen giɓi a zukatan mu ya'yan ta, la'akari da tsafta ciyar rayuwar da ta yi me cike da bautar Allah maɗaukakin Sarki, zikiri, zumunci da kuma halin ta na son jama'a.
"A madadin ɗaukacin al'ummar jihar Bauchi, gwamnati da iyalai na, ina miƙa ta'aziyya ga babban yaya na Wali da yan uwa da abokai bisa wannan rashi, tare da addu'ar Allah ya gafarta mata ya sanya ta cikin dausayin Aljanna. Amin."

Mahaifiyar Gwamna Radda ta bar duniya

A baya, kun ji cewa an shiga jimami a jihar Katsina sakamakon rasuwar Hajiya Safara’u Umar Radda, mahaifiyar Gwamna Dikko Radda, a ranar Lahadi 23 ga Maris, 2025.

An tabbatar da cewa Hajiya Safara’u ta rasu bayan ta sha fama da doguwar jinya kamar yadda Isah Miqdad, ya tabbatar.

Isah Miqdad ya bayyana cewa marigayiyar ta yi fama da jinya kafin rasuwarta inda ya roki Allah ya jikan marigayiyar, tare da yi mata addu'ar rahama da samun gafara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.