Kamfanin da Buhari Ya Kaddamar Ya Fara Hada Kayan Sola da Robobi a Borno
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya kai ziyarar duba masana’antar jihar da ta ke kera abubuwa biyar
- An kafa kamfanin ne ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jihar da masu zaman kansu domin farfaɗo da tattalin arzikin Borno
- Gwamnatin jihar na gudanar da aikin hanyoyi na Naira biliyan 11 da kuma sola ta Naira biliyan 5 domin inganta ayyukan kamfanin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya kai ziyarar duba aiki a cibiyar masana’antu ta jihar da ke kan hanyar Maiduguri–Kano.
Ziyarar na cikin shirin gwamnan na farfaɗo da masana’antu da kuma dawo da cigaban tattalin arzikin jihar da ya daɗe yana durƙushe sakamakon rikicin Boko Haram.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai kan kamfanin hada kayan roba kala-kala ne a jihar a wani sako da hadimin gwamna Zulum, Dauda Iliya ya wallafa a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masana’antar da ke aiki ƙarƙashin tsarin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, na ɗaya daga cikin manyan ginshiƙai na shirin Zulum na samar da ayyuka.
Gwamnatin jihar ta fara gina sabuwar hanya mai darajar Naira biliyan 11 da kuma tashar wutar sola da ta kai Naira biliyan 5 domin tabbatar da cewa cibiyar za ta yi aiki da cikakken ƙarfin ta.
Kayayyaki 5 da ake yi a kamfanin Borno
Cibiyar masana’antu ta Borno tana da sassa guda biyar da ke samar da kayayyaki daban-daban, ciki har da kujeru, bokiti da kofuna, bututun ruwa (pipe), buhuna, da kayan wutar sola.
Rahotanni sun nuna cewa a kullum ana samar da buhuna 100,000, bututun ruwa 18,500, wadanda ke nuni da cewa masana’antar na aiki sosai.

Kara karanta wannan
Najeriya ta yi wa Trump martani mai zafi kan zargin kashe Kiristoci, ta ce karya ne
Ana ganin cigaban wata alama ce ta hangen nesan gwamnatin Borno wajen farfaɗo da masana’antu da ƙirƙirar hanyoyin samun kuɗin shiga ga jihar bayan fama da matsalar tsaro.
Yaushe Buhari ya kaddamar da kamfanin?
Mai taimakawa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, ya bayyana cewa yanzu jihar Borno ta fara fitar da kayayyakin roba zuwa wasu sassan ƙasar nan.
A sakon da ya wallafa a X, Bashir ya ce masana’antar da Muhammadu Buhari ya ƙaddamar a watan Afrilu 2019 yanzu tana aiki da cikakken ƙarfin ta.

Source: Facebook
'Tattalin arzikin Borno zai habaka,' Bashir Ahmaad
Bashir ya ce kamfanin babbar nasara ce ga jihar, inda ya ce shirin zai rage dogaro da gwamnatin tarayya da kuma buɗe damar kasuwanci ga jama’ar Borno.
Ya kara da cewa:
“Farfesa Zulum yana canza fuskar tattalin arzikin jihar. Wannan masana’anta za ta taimaka wajen samar da dubban ayyukan yi, rage fatara, da kuma dawo da martabar jihar a harkar masana’antu.”
Maganar Zulum kan mata Musulmi
A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin jihar Borno ta yi magana kan zargin keta hakkin mata Musulmai a wasu asibitoci.

Kara karanta wannan
Yadda farashin fetur zai kasance bayan Tinubu ya amince da harajin 15% a Najeriya
Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayar da umarnin yin cikakken bincike kan zargin hana mata sanya hijabi a asibitoci.
Farfesa Zulum ya ce jihar Borno tana mutunta addinin al'umma tare da kiyaye hakkin mata, saboda haka ba za ta lamunci cin zarafi ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
