An Gargadi Shugabanni da Talakawa kan Mulkin Soja a Najeriya

An Gargadi Shugabanni da Talakawa kan Mulkin Soja a Najeriya

  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya ce babu wani amfani da zai fito daga mulkin soja
  • 'Dan siyasar ya bayyana hakan ne yayin da yake martani kan rade-radin yunƙurin juyin mulki da ake yadawa a ƙasar nan
  • Adebayo ya ce dole ne gwamnati ta bayyana gaskiya ga ‘yan ƙasa domin tabbatar da amincewar jama’a ga dimokuraɗiyya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya bayyana cewa komawa mulkin soja a Najeriya ba zai haifar da wani alheri ba.

Ya yi magana yana mai cewa duk wata tafiyar da za ta rushe tsarin dimokuraɗiyya abin ƙyama ce a halin yanzu.

Adewole Adebayo, Bola Tinubu
Adewole Adebayo tare da shugaba Bola Tinubu. Hoto: @Pres_Adebayo|@aonanuga1956
Source: Facebook

Adebayo ya faɗi haka ne a ranar Alhamis yayin wata hira da aka yi da shi a Channels TV, inda ya yi martani kan rade-radin yunƙurin juyin mulki da ya tayar da hankula a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Rajistar jam'iyyu: INEC ta fadi kungiyoyi 8 da suka tsallake zuwa mataki na gaba

Ya ce dole ne duka bangarorin soja da na farar hula su fito fili su bayyana gaskiya kan abin da ya faru, domin hakan ne kawai zai tabbatar da amincewar jama’a ga tsarin gwamnati.

Adebayo ya nemi a kare mulkin dimokuraɗiyya

Adebayo ya bayyana cewa tsarin dimokuraɗiyya na fuskantar barazana a yanzu, don haka ya kamata a kula da shi domin gudun rugujewa.

Ya ce hanya mafi kyau ta kare ƙasa daga juyin mulki ko rikicewar doka ita ce kyakkyawan mulki da gaskiya ga jama’a.

A cewarsa:

“Dimokuraɗiyya na cikin hadari, sojoji na ƙoƙarin rusa ta a wasu wurare, a wasu kuma ba a ba jama’a ‘yancin yin zaɓe cikin gaskiya.

Ya ƙara da cewa yayin da ake jiran sojoji da hukumomin farar hula su fito da cikakken bayani, babban darasin da ake bukatar koya shi ne muhimmancin kiyaye tsarin dimokuradiyya.

Gargadin Adebayo ga shugabannin Najeriya

Adebayo ya gargadi shugabannin siyasa cewa babu wanda yake da cikakkiyar kariya daga rikici ko rashin tabbas.

Kara karanta wannan

Yadda farashin fetur zai kasance bayan Tinubu ya amince da harajin 15% a Najeriya

Adewole Adebayo
Adebayo Adewole yayin wani taron siyasa. Hoto: @Pres_Adebayo
Source: Facebook

Ya ce kamar yadda talakawa ke fuskantar rashin tsaro a rayuwa da dukiyoyinsu, haka ma masu mulki za su iya fuskantar rashin tabbas a kujerunsu idan suka kasa kula da jama’a.

“Darasin da ya kamata a koya shi ne mu ji tausayin jama’a, mu saurari ƙorafin su, mu tabbatar da cewa suna samun abin da ya dace,”

Inji shi

The Cable ta rahoto ya kara da cewa:

“Ni na taso ƙarƙashin mulkin soja tun a lokacin Gowon, kuma na yi gwagwarmaya da tsarin soja a matsayina na ɗan gwagwarmaya — babu wani alheri da zai fito daga mulkin soja.”

Tinubu ya sauya shugabannin tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da manyan sauye-sauye a cikin jagorancin rundunar sojojin Najeriya.

A cikin sauye-sauyen, Manjo Janar Waidi Shaibu ya maye gurbin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin sabon shugaban sojojin kasa.

Kara karanta wannan

'Tinubu zai rika karbar harajin shakar iska a Najeriya,' 'Dan takarar Shugaban Kasa a SDP

Majalisar kasa ta tantance shugabannin tsaro kuma tuni Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya karbi ragamar shugabancin rundunar tsaro ta kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng