Sanata Natasha: Abin da Ya Sa Na Gayyaci Akpabio wajen Kaddamar da Aikina a Kogi
- Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana dallilinta na gayyatar Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio zuwa Kogi
- A zaman majalisa na ranar Alhamis, Sanata Natasha ta gayyaci Akpabio da wasu ‘yan majalisar dattawa zuwa ƙaddamar da ayyukanta a Kogi
- Natasha Akpoti-Uduaghan ta mika goron gayyatar ne watanni biyu bayan dawowarta daga dakatarwar da majalisa ta yi mata na tsawon watanni
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja – Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta kare kanta a kan gayyatar da ta yiwa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio.
A ranar Alhamis ne Natasha ta gayyaci Akpabio da wasu ‘yan majalisa zuwa ƙaddamar da ayyuka a jihar watanni kadan da dawowarta bakin aiki.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa ta rubuta wasika ga majalisar wanda Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya karanta a zauren majalisa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Natasha ta fadi dalilin gayyatar Akpabio
Jaridar Daily Post ta wallafa cewa gayyatar da ta yiwa Sanata Godswill Akpabio da sauran 'yan majalisa kamar yadda al’ada ta tsara.
Ta kara da cewa:
“Na aika da gayyatar ne don kada a dauka ina biki ni kadai. Ni mutum ce mai hangen nesa. Ko da akwai shari’o’in da ake yi, ina ci gaba da aiwatar da aikina a majalisar da bin dukkannin matakai."

Source: Facebook
Tun dawowarta daga dakatarwa a ranar 24 ga Satumba 2025, Sanata Akpoti-Uduaghan ta fara shiga ayyukan majalisa a hankali.
A ranar Alhamis, ta kuma gabatar da kudiri da nufin kafa cibiyoyin kula da yara masu bukata ta musamman dake dauke da cutar 'autism' a kasa da shiyyoyin guda shida a fadin Najeriya.
Kudirin zai tallafa wajen gano cutar tun da wuri, bincike, da kula da mutanen da ke da cutar ta ASD a fadin kasar.
Sanata Natasha ta girmama 'yan majalisa
Sanata Natasha ta kara da cewa wannan mataki yana nuna girmamawa ga tsarin doka da majalisa, tare da nuna cewa babu ruwan aiki da bukatar kashin kai.
Wannan na zuwa ne bayan rigimar ta da Akpabio a watan Fabrairu game da matsayi a majalisa, inda daga bisani ta zargi shugaban majalisar da cin zarafinta.
Bayan wannan zargi nce kuma majalisa ta dakatar da Sanata Natasha na tsawon watanni shida daga majalisa a watan Maris.
Majalisa ta amince da kafa jihohi
A baya, mun wallafa cewa kwamitin haɗin gwiwa na majalisar dattawa da majalisar wakilai kan sake duba kundin tsarin mulki ya amince da kirkiro karin jihohi guda shida a kasar nan.
Wannan babban mataki ya zo ne a karshen taron bita na kwanaki biyu da aka yi Legas, karkashin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin da Rt. Hon. Benjamin Kalu.
A yayin taron, kwamitin ya tattauna kudirori 69, bukatu 55 na kirkirar jihohi, bukatu biyu na gyaran iyaka, da bukatu 278 na kirkirar kananan hukumomi a daga sauran jihohin kasarnan daban-daban.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

