'Tinubu zai Rika Karbar Harajin Shakar Iska a Najeriya,' 'Dan Takarar Shugaban Kasa a SDP

'Tinubu zai Rika Karbar Harajin Shakar Iska a Najeriya,' 'Dan Takarar Shugaban Kasa a SDP

  • 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a 2023, Adewole Adebayo, ya soki matakin Bola Tinubu na saka haraji a kan mai
  • Adewole Adebayo ya ce matakin ya nuna yadda gwamnatin shugaba Bola Tinubu ke neman kudi daga 'yan kasa ta kowace hanya
  • 'Dan siyasar ya bukaci shugaban kasa da ya gyara matatun man Najeriya da suka dade ba su aiki kafin tunanin ƙarin harajin 15%

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – 'Dan takarar shugaban kasa a SDP a 2023, Adewole Adebayo, ya caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu a kan amincewa da harajin 15% kan shigo da fetur da dizil.

Ya ce gwamnatinTinubu ta zama mai tsauri wajen saka haraji ga jama’a, tana neman hanyoyi daban-daban na karɓar kuɗi daga talakawa.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta fitar da gargadi kan yada labaran yi wa Tinubu juyin mulki

Shugaban kasa Bola Tinubu
Shugaba Tinubu da jagoran SDP, Adebayo. Hoto: @Pres_Adebayo|@aonanuga1956
Source: Twitter

Adebayo ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar Channels Television a daren Alhamis, inda ya kira wannan mataki “tsarin danniya da rashin tausayi.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Tinubu zai karbi harajin shakar iska” – Adebayo

Adebayo ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin “mai kwarewa wajen karɓar haraji,” yana mai cewa idan aka barshi, zai iya saka haraji kan iska da mutane ke shaka.

Ya ce:

“Shugaba Tinubu ya iya tara haraji. Nan gaba kadan, zai fara karɓar harajin iska da muke shaka. Idan ba a kula ba, zai aikata.”

Adebayo ya ci gaba da cewa wannan sabon harajin ya sabawa manufofin da Tinubu ya tsaya a kai a baya lokacin da yake cikin SDP tare da Abiola, yana fafutukar manufofin Hope 93.

“Ina mamakin yadda Tinubu ya canza daga bangaren talakawa zuwa bangaren masu kudi.
"A yanzu, yana kallon mutane a matsayin abubuwan kasuwanci, ba ’yan ƙasa ba,”

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani bayan Tinubu ya sassauta hukuncin Maryam Sanda

- Inji shi

Adebayo ya fadi illolin harajin 15% kan mai

'Dan siyasar ya bayyana cewa sabon harajin zai ƙara wa ‘yan Najeriya nauyi, musamman ganin yadda ake fama da matsin tattalin arziki.

Shugaba Bola Tinubu
Shugaban kasa Bola Tinubu na jawabi a taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya kara da cewa:

“Idan aka saka harajin kashi 15 cikin 100 a kan shigo da mai, wa zai biya? Talaka ne a tashar mai zai biya ta hanyar karin farashi,”

Ya kara da cewa gwamnati na aikata kuskure kuma ba ta yi wa jama’a adalci, domin tana neman kuɗi daga talakawa maimakon gyara matsalolin cikin gida.

Bukatar gyara matatu kafin karin haraji

Adebayo ya soki gwamnati saboda gazawar da ta yi wajen tabbatar da cewa matatun mai na cikin gida sun fara aiki yadda ya kamata.

Ya kara da cewa:

“Ya kamata shugaban kasa ya kira Heineken Lokpobiri da Bayo Ojulari ya ce musu ‘ina so matatun nan su fara aiki cikin wata shida.’”

Kara karanta wannan

Kashim Shettima ya aika sako ga dattawan Arewa kan batun raba Najeriya

Shigo da mai: Tinubu ya saka harajin 15%

A baya, mun rahoto cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da saka harajin 15% ga duk wanda zai shigo da mai da dizil zuwa ƙasar nan.

Matakin, wanda shugaban hukumar FIRS Zacch Adedeji ya gabatar, ya ce yana da nufin kare matatun cikin gida da kuma daidaita kasuwar man fetur.

Bincike ya nuna cewa Najeriya tana shigo da kusan kashi 67 na man fetur, yayin da ake samar da ƙasa da kashi 40 a cikin gida, musamman daga matatar Dangote.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng