Maryam Sanda: Lauya Ya Ci Gyaran Tinubu, Ya Fadi Kuskuren da Ya Kuma Yi

Maryam Sanda: Lauya Ya Ci Gyaran Tinubu, Ya Fadi Kuskuren da Ya Kuma Yi

  • Wani lauya ya yi magana kan kuskuren da Bola Ahmed Tinubu ya yi game da janye afuwa da ya yi ga wasu mutane 86
  • Frank Tietie ya ce Tinubu bai da ikon soke afuwa bayan an riga an bayar da ita bisa doka, ciki har da ta Maryam Sanda
  • Ya jaddada cewa ba a dawo da ikon afuwa baya, kuma shugaban kasa ba zai iya sake hukunta ko canza hukuncin wadanda aka yafewa ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani lauya kuma mai sharhi kan harkokin jama’a ya fadi kuskuren da Bola Tinubu ya yi kan janye afuwa ga su Maryam Sanda.

Lauya Frank Tietie ya bayyana cewa Tinubu bai da ikon soke afuwa idan an riga an bayar da ita bisa doka inda ya kawo hujjoji kan haka.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani bayan Tinubu ya sassauta hukuncin Maryam Sanda

Lauya ya gano kuskuren Tinubu kan lamarin Maryam Sanda
Marigayi Bilyaminu Bello, Maryam Sanda da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Matsayar lauya kan janye afuwar da Tinubu ya yi

Tietie ya yi wannan bayanin ne a ranar Alhamis 30 ga watan Oktobar 2025 a hirar sa da gidan jaridar ARISE News.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya mayar da martani kan matakin Shugaba Tinubu na janye afuwar da aka bai wa wasu fursunoni, ciki har da Maryam Sanda wadda aka sauya hukuncinta zuwa shekaru 12 a gidan yari.

A cewarsa, ikon bayar da afuwa ikon ne na karshe, kuma idan shugaban kasa ya sanya hannu ya kammala aiwatar da shi, ba shi da hurumin janye shi kuma.

Ya ce:

“A lokacin da shugaban ya rattaba hannu a karon farko, aikin ya kammala. Babu ikon da zai mayar da shi baya. An riga an karɓa.”

Lauyan ya kara da cewa shugaban kasa ba shi da ikon hukunta mutum ko sake hukunci, don haka ba zai iya cewa wanda aka yafewa bai dace ba bayan an yi afuwar.

Kara karanta wannan

Lauya ya fadi lokacin da ya ragewa Maryam Sanda a kurkuku sakamakon afuwar Tinubu

“Shugaban kasa ba alkali ba ne. Ba zai iya daukar ikon kotu ba ta hanyar soke afuwa bayan an yanke hukunci.”

- Frank Tietie

Wani lauya mai suna Hussaini Hussaini ya bayyana irin haka a shafinsa na Facebook a yammacin ranar Laraba.

Barista Hussaini da ke aiki a Dikko & Mahmoud ya ce shugaban kasa yana da ikon afuwa, amma bai da ikon soke afuwar da ya yi.

Lauya ya shawarci Tinubu kan halin kunci da ake ciki
Shugaba Bola Tinubu yayin jawabi a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Lauya ya ba Tinubu shawara kan cire tallafi

Bugu da kari, Tietie ya ce gwamnati mai sauraron jama’a ya kamata ta yi la’akari da halin mutane, da ta waiwayi batun cire tallafin mai da kara kudin wutar lantarki.

A cewarsa, cire tallafin mai da karin kudin wuta sun kara takura rayuwar al’umma, kuma akwai bukatar gwamnatin ta yi tunani mai zurfi kan irin wadannan manufofi.

Matakin Shugaba Tinubu na janye afuwar da aka bayar a baya ya ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, musamman kan ikon shugaban kasa karkashin sashe na 175 na kundin tsarin mulki na 1999 da aka yi wa kwaskwarima.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda

An fadi dalilin rangwame ga Maryam Sanda

Kun ji cewa Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi SAN, ya bayyana dalilin sassauci ga Maryam Sanda da sauran wadanda aka daure.

Fagbemi ya ce gwamnatin Tinubu ta yi rangwame a hukuncin wasu fursunoni 86 ciki har da Maryam Sanda saboda cancantarsu.

Kotu ta yankewa Maryam hukuncin kisa a 2020 bayan ta kashe mijinta, amma yanzu an mayar da hukuncin zuwa shekara 12 a gidan kaso.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.