Lauya Ya Fadi Lokacin da Ya Ragewa Maryam Sanda a Kurkuku sakamakon Afuwar Tinubu

Lauya Ya Fadi Lokacin da Ya Ragewa Maryam Sanda a Kurkuku sakamakon Afuwar Tinubu

  • Fitaccen lauya, Abba Hikima ya ce a tsarin gidan yari, shekara guda ba watanni 12 bane kamar yadda aka sani a rayuwar yau da kullum
  • Ya bayyana haka ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sassauta hukuncin kisa da kotunan kasar nan suka yanke wa Maryam Sanda
  • Barista Abba Hikima ya bayyana cewa Maryam Sanda ta kusa cika wa'adin da aka yanke mata bayan da shugaba Bola Tinubu ya sassauta hukunci

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Fitaccen lauya mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Abba Hikima, ya yi yi lissafin wa'adin da ya ragewa Maryam Sanda a gidan yari.

Wannan na zuwa ne bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sassauta mata hukunci daga na kisa zuwa zaman kurkuku na shekaru 12 bayan ta kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito fili: Gwamnatin Tinubu ta faɗi dalilin sassauci ga Maryam Sanda

Abba Hikima ya lissafa lokacin da ya ragewa Maryam Sanda a kurkuku
Hoton Barista Abba Hikima, da Maryam Sanda Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook Abba Hikima ya bayyana cewa wannan sassauci na nufin saura kadan Maryam Sanda ta shaki iskar 'yanci kamar kowa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Maryam Sanda na dab da barin kurkuku

Barista Abba Hikima ya bayyana cewa lissafin tsarin gidan yari na Najeriya, shekara guda ba daidai yake da watanni 12 ba.

Ya ce a lissafin zaman gidan kaso, shekara daya na nufin mutum zai yi zaman watanni takwas ne kacal ba watanni 12 ba.

Saboda haka, bisa wannan lissafi, Maryam Sanda wadda ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yari, ta riga ta yi kusan shekaru 10 a ma’aunin gidan yari.

Abba Hikima ya ce bayan shugaban ƙasa ya rage mata hukunci zuwa shekaru 12, hakan na nufin cewa yanzu saura kusan kimanin watanni 16 ta kammala zaman gidan yari.

Ya ƙara da cewa:

"A lissafin gidan yari, shekara daya ba watanni 12 bace, kimanin watanni takwas ne. Saboda haka, tunda Maryam Sanda ta shafe cikakkun shekaru 6 da watanni 8 din da Maryam Sanda a gidan yari, idan aka juya su zuwa shekarun gidan yari, zai kai kusan shekaru 10."

Kara karanta wannan

Bayan soke afuwa, Tinubu ya sassauta hukuncin kisan da aka yanke wa Maryam Sanda

Jama'a sun yi tir da sassautawa Maryam Sanda

Sai dai Abba ya tunatar cewa bayan hukuncin duniya akwai hukuncin lahira, yana mai cewa nan da shekara daya da watanni hudu.

Ya kara da cewa:

“Sai dai bayan hukuncin duniya akwai na kiyama.”
Abba Hikima ya yi tir da rage hukuncin Maryam Sanda
Hoton fitaccen lauya a Kano, Barista Abba Hikima Hoto: Abba Hikima
Source: Facebook

Wasu masu bibiyar shafin na Abba Hikima sun bayyana ra'ayinsu a kan sassaucin da aka yi wa Maryam Sanda, musamman idan aka yi la'akari da laifin da ta aikata.

Wani Abubakar MK Gwantu ya bayyana cewa:

“Kai haba, yanzu dai ta kashe wofi kenan Barista?”

Nura Usman kuma ya bayyana cewa:

“Aƙalla wannan ya fi wancan rashin kunyar da aka yi mata na sakin ta kai tsaye.”

Ahmed Baba Ahmed ya ce:

“Alhamdulillah, akwai rayuwa bayan mutuwa. Kowa zai girbi abin da ya shuka, kuma babu wanda za a zalunta a ranar.”

Usman Zakari Ibrahim ya ce:

“Subhanallahi, muna roƙon Allah ya nuna ikonsa da ƙarfin sa a wannan lamari.”

Tinubu ya sassautawa Maryam Sanda

Kara karanta wannan

Mutanen birnin tarayya za su zauna a duhu, TCN ya fadi dalilin dauke wuta a Abuja

A baya, mun wallafa cewa ofishin mai magana da yawun shugaban ƙasa ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake duba jerin waɗanda zai yi wa afuwa.

Daga cikin waɗanda aka sake duba lamarinsu akwai Maryam Sanda — wacce kotu ta yanke masa hukuncin kisa bisa laifin hallaka mijinta, Bilyaminu Bello a gidansu.

A wannan karon, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya rage mata hukunci, inda aka kawar da hukuncin kisa da aka yanke mata zuwa zaman kurkuku na tsawon shekaru 12.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng