Gwamna Dauda Ya Fadi Matsalar Sulhu da 'Yan Bindiga, Ya Yi Gargadi

Gwamna Dauda Ya Fadi Matsalar Sulhu da 'Yan Bindiga, Ya Yi Gargadi

  • Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi tsokaci kan suhun da ake da 'yan bindiga a wasu yankunan Arewacin Najeriya
  • Dauda Lawal ya yi gargadin cewa sulhun da ke barin 'yan bindiga da mugayen makamansu bai kawo karshen rikici
  • Hakazalika, gwamnan ya bayyyana matsalolin da suka jawo ake samun rashin tsaro a jiharsa ta Zamfara

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi gargadi kan hawa teburin sulhu da ake yi da 'yan bindigan da ke dauke da makamai.

Gwamna Dauda ya yi gargadin cewa sulhun da ke barin kungiyoyin ‘yan bindiga da makaman su tare da ba su damar sa sharudda, bai magance tashin hankali, illa dai jinkirta rikici da raunana ikon gwamnati.

Gwamna Dauda ya yi magana kan sulhu da 'yan bindiga
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakinsa, Sulaiman Bala Idris, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Taraba: Gwamna ya ba da umarni kan rigimar masallacin Juma'a da aka rasa rai

Me Dauda ya ce kan sulhu da 'yan bindiga?

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake gabatar da lacca ga mahalarta taron Executive Intelligence Management Course (EIMC) 18 a cibiyar NISS da ke Abuja.

Mahalarta taron sun haɗa da jami’ai daga muhimman hukumomin tsaro na Najeriya da kuma wasu kasashen Afirka irin su Chad, Ghana, Rwanda, Somalia, da Gambia.

Gwamna Dauda Lawal ya yi gargadin cewa shirye-shiryen sasanci marasa tsari a wasu sassan Arewa maso Yamma suna iya zama barazana ga tsaron kasa.

“Tattaunawa na iya taimakawa wajen rage rikici, amma zaman lafiya na gaskiya ba zai tabbata ba sai da kwace makamai da sulhu na gaskiya."
“Barin kungiyoyin ‘yan bindiga da makaman su yayin da suke sa sharuddan zaman lafiya, yana nufin jinkirta tashin hankali da rage karfi da ikon gwamnati."
"A wannan lokaci mai muhimmanci, dole zaman lafiya ya kasance karkashin jagorancin gwamnati, tare da tsari mai karfi da goyon bayan doka."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace masu ibada 20, sun hallaka malamin addini a Kaduna

"Dole gwamnati ta nuna tana da karfin iko da kuduri wajen tabbatar da zaman lafiya.”

- Gwamna Dauda Lawal

Gwamnan ya yi magana kan tsaron Zamfara

Gwamnan ya ce abubuwan da ke faruwa a Zamfara, suna nuna irin kalubalen da ake fuskanta a sassa da dama na Najeriyada ma nahiyar Afirka baki ɗaya wajen neman zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Dauda Lawal ya yi tsokaci kan sulhu da 'yan bindiga
Gwamna Dauda Lawal na jawabi a wajen taro Hoto: Mugira Yusuf
Source: Facebook

Ya danganta matsalolin tsaron jihar da talauci mai tsanani, kokuwa kan albarkatun kasa, sauyin yanayi, yawaitar makamai da rashin aikin yi ga matasa.

“Da muka hau mulki a 2023, mun ɗauki tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a matsayin babban abin da ya fi muhimmanci."
"Sai dai ingantaccen tsaro ba zai samu ba sai da goyon bayan jama’a.”

- Gwamna Dauda Lawal

Wani mazaunin Kankara a jihar Katsina, Idris Hussain, ya shaidawa Legit Hausa cewa tabbas bai kamata ana sulhu da 'yan bindiga ba tare da kwace makamansu ba.

"Ai kamar kashe maciji ne ba tare da sare masa kai ba. Mutanen nan ba tuban kirki suke yi ba. Sulhu na gaskiya shi ne su daina ta'addanci sannan su ajiye makamansu."

Kara karanta wannan

Kwamandojin 'yan bindiga sun kaure da fada, shedanin dan ta'adda ya sheka barzahu

"Ko an yi sulhun da su zuwa wani dan lokaci sai su dawo ruwa."

- Idris Hussain

'Yan bindiga sun kashe mutane a masallaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan masallata a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Na'alma da ke karamar hukumar Malumfashi lokacin da mutane suke sallar Asuba.

Harin ya jawo asarar rayukan mutane da dama tare da raunata wasu daban wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng