CDCFIB Ta Saki Sunan Wadanda aka Zaba a Neman Aikin NIS, NSCDC, Hukumomi 2

CDCFIB Ta Saki Sunan Wadanda aka Zaba a Neman Aikin NIS, NSCDC, Hukumomi 2

  • Hukumar CDCFIB ta saki jerin sunayen waɗanda suka cancanci cigaba zuwa mataki na gaba shirin daukar aiki
  • An shawarci masu neman aikin su fara duba sunayensu ta shafin hukumar daga yau Alhamis, 30, Oktoba, 2025
  • Hukumar ta gargadi jama’a da su guji shafukan bogi da ke yaudarar masu neman aiki da sunan cewa sun samu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar CDCFIB ta sanar da sakin jerin sunayen waɗanda suka samu shiga matakin gaba na daukar ma’aikata a cikin hukumomin tsaron kasa.

Sanarwar ta hada da wadanda suka nemi aiki a hukumar NCoS, hukumar shige da fice ta kasa (NIS), hukumar kashe gobara FFS, da kuma hukumar tsaro NSCDC.

Wasu jami'an hukumomin NSCDC, NIS
Jami'an wasu daga cikin hukumomin da za a dauki ma'aikata. Hoto: Zagazola Makama
Source: Twitter

Sanarwar na kunshe ne cikin wata takarda da sakatare ga hukumar, Manjo Janar A.M. Jibril (Mai ritaya) ya sanya hannu a kai, wacce aka wallafa a shafin X na CDCFIB.

Kara karanta wannan

Anambra 2025: Manyan laifuffukan zabe a Najeriya da hukuncin da doka ta tanada

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda za a duba sunaye a shafin CDCFIB

A cewar sanarwar, duk wadanda suka nemi aiki a wadannan hukumomi za su iya ziyartar shafin hukumar a nan daga ranar Alhamis, 30, Oktoba, 2025.

Za su ziyarci shafin ne domin duba ko sun shiga cikin jerin sunayen wadanda aka zaba domin zuwa mataki na gaba.

Jibril ya ce an umarci wadanda sunayensu suka fito da su tabbatar da bayanan wurin da suka rubuta jarabawar kwamfuta (CBT), rana da lokaci kamar yadda aka wallafa a shafin.

Ya kara da cewa an tsara jarabawar ne cikin gaskiya da adalci domin tabbatar da cewa kowa ya samu daidai da cancantarsa.

Gargaɗin CDCFIB ga masu neman aiki

Manjo Janar Jibril ya gargadi masu neman aiki da su yi hattara da wasu ‘yan damfara da shafukan yanar gizo na karya da ke ikirarin wakiltar hukumar.

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa ya jaddada cewa shafin hukumar da aka ambata shi ne kadai tushen sahihin bayani da ake amfani da shi wajen daukar ma’aikata.

Kara karanta wannan

Rubutu a Facebook ya jefa 'yan Kwankwasiyya 2 a gagarumar matsala a Kano

“Ana shawartar duk masu nema da su kula da adireshin hukumar da aka nuna don kauce wa fadawa tarkon masu zamba,”

Inji shi.

Jami'an NSCDC a Abuja
Wasu jami'an NSCDC a bakin aiki. Hoto: @official_NSCDC
Source: Twitter

Haka kuma, hukumar ta bayyana cewa duk wani wanda aka samu da hannu wajen yaudara ko karɓar cin hanci zai fuskanci hukunci mai tsanani.

CDCFIB ta ce za ta duba cancanta

Sakataren ya tabbatar da cewa hukumar CDCFIB ta kuduri aniyar gudanar da aikin daukar ma’aikata cikin gaskiya da bin ka’ida.

Ya ce manufar hukumar ita ce cike gibin karancin ma’aikata a hukumomin domin inganta tsaron kasa da kuma inganta rayuwar jama’a.

Hukumar ta bayyana cewa za ta ci gaba da daukar matakai na tabbatar da inganci da daukar ma’aikatan da ke da kwarewa da kishin kasa.

Legit ta tattauna da mai neman aiki

A tattauna wa da Legit Hausa, wani matashi da ya ke neman aikin ya tabbatar da cewa sunan shi ya fito da ya duba.

Hamza Abdullahi ya ce:

"Na yi farin ciki bayan ganin suna na. Ina fatan za su yi gaskiya wajen tantance mutane da jarrabawar da za a yi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi wa shugabannin al'umma 2 yankar rago a jihar Katsina

'Ina neman aikin NSCDC ne, kuma ina fatan zan samu da yardar Allah."

Dangote zai dauki 'yan Najeriya aiki

A wani labarin, mun kawo muku cewa Alhaji Aliko Dangote ya fara shirin fadada matatarsa zuwa mafi girma a duniya.

Dangote ya tabbatar da cewa zai dauki ma'aikata da dama domin fadada matatar kuma mafi yawansu za su fito ne daga Najeriya.

Attajirin ya bayyana haka ne yayin wani zama da ya yi da manyan jami'an matatar a makon da ya wuce a jihar Legas.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng