Gwamnati Ta Fayyace Gaskiya kan Batun Boyayyen Filin Jirgin Sama a Kebbi
- An yada wani faifan bidiyo da ya yi ikirarin cewa akwai wani filin jirgin sama da ke amfani da shi don safarar hodar iblis a Kebbi
- Gwamnatin jihar Kebbi ta fito ta yi bayani mai gamsarwa kan zargin wanda aka yada a shafuka da kafofin sada zumunta
- Mai ba Nasir Idris shawara kan harkokin yada labarai ya bayyana cewa filin jirgi guda daya ne kawai ake da shi a fadin jihar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta yi martani kan rahotannin da ke nuna cewa akwai wani filin jirgin sama da ake amfani da shi don safarar hodar iblis.
Gwamnatin Kebbi ta karyata faifan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke zargin cewa akwai wani filin jirgin sama a cikin dajin Argungu da ake amfani da shi wajen safarar hodar iblis.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mai ba Gwamna Nasir Idris shawara kan harkokin yada labarai, Malam Yahaya Sarki, ya fitar ranar Laraba a Birnin Kebbi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me gwamnati ta ce kan filin jirgin saman?
Gwamnatin ta bayyana cewa gaba daya abin da ke cikin bidiyon karya ne, kuma an kirkire shi ne domin bata suna da ɓata martabar gwamnati.
“Dukkan abin da ke cikin bidiyon karya ne kuma yaudara ce kawai da aka shirya."
"Babu wani lamari da ya taɓa faruwa na safarar miyagun kwayoyi ko wani filin jirgin sama da ake amfani da shi ba bisa ka’ida ba a karamar hukumar Argungu ko wani yanki na jihar Kebbi."
- Mallam Yahaya Idris
Ya bayyana cewa filin sama na kasa da kasa na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi shi ne kawai filin jirgin da ke aiki a jihar, za a samu labarin a rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan
Nasara daga Allah: Yan bindiga sama da 80 sun bakunci lahira da suka yi yunkurin shiga Kebbi
Hakazalika ya bayyana cewa Argungu ba ta da filin jirgin sama, wurin tashin jirgi ko wani abu makamancinsu.
Yahaya Sarki ya kara da cewa dukkan sunaye da mutanen da aka ambata a bidiyon na bogi ne, babu su a zahiri.
Ya kuma ce babu wata hukumar tsaro kamar Kwastam, NDLEA, ko wata hukuma da ta gudanar da bincike kan irin wannan zargi.

Source: Original
An bukaci jama'a su yi watsi da batun
Hakazalika ya bukaci jama’a su yi watsi da wannan labarin na karya, yana mai cewa an kirkire shi ne domin ruɗar da mutane da haifar da tashin hankali a tsakanin al’umma.
“Gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris na ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da gaskiya, ingantaccen mulki da haɗin gwiwa da dukkan hukumomin tsaro da na yaki da miyagun kwayoyi na tarayya."
- Mallam Yahaya Sarki
Gwamnan Kebbi ya yi garambawul a gwamnati
A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yi wani dan karamin garambawul a gwamnatinsa.
Mai girma Gwamna Nasir Idris ya sauyawa wasu kwamishinoni biyu na gwamnatinsa ma'aikatun da za su jagoranta.
Ya bayyana cewa sauyin na daga cikin manufar gwamnatinsa na inganta harkokin mulki domin jindadin mutanen jihar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

