Bakary: Za a Gurfanar da Dan Adawar Kamaru da Ya Buga Takara da Paul Biya

Bakary: Za a Gurfanar da Dan Adawar Kamaru da Ya Buga Takara da Paul Biya

  • Gwamnatin Kamaru ta ce za ta dauki matakin shari’a kan jagoran adawa, Issa Tchiroma Bakary bisa zargin tayar da tarzomar bayan zabe
  • Akalla mutane hudu aka kashe yayin arangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan 'yan adawa tun bayan zaben shugaban kasa
  • Ministan cikin gida Paul Atanga Nji ya ce wasu daga cikin masu taimaka wa Bakary wajen shirya tarzomar ma za su fuskanci hukunci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Cameroon – Ministan cikin gida na Kamaru, Paul Atanga Nji, ya bayyana cewa gwamnati za ta gurfanar da jagoran 'yan adawa, Issa Tchiroma Bakary a gaban kotu.

Za a gurfanar da Bakary ne bisa zargin shiryawa da tayar da tarzomar da ta biyo bayan zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga Oktoba, 2025.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II zai jagoranci taron duniya a gaban gwamnoni da ministoci

Paul Biya, Issa Bakary
Shugaba Paul Biya da jagoran adawa a Kamaru. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta wallafa cewa a kalla mutane hudu ne suka rasu yayin da jami’an tsaro suka yi arangama da magoya bayan 'yan adawa a birane daban-daban bayan sanar da sakamakon zaben.

Za a gurfanar da dan adawan Kamaru a kotu

Paul Atanga Nji ya zargi Tchiroma Bakary da shirya zanga-zangar da ta janyo asarar rayuka da dukiya ba tare da izini ba.

A kan haka ne za a gurfanar da Bakary da “abokan aikinsa” da ake zargi da hannu bisa zargin tayar da zaune tsaye.

A cewarsa, gwamnatin Kamaru ba za ta lamunci duk wani yunkuri na kawo rudani ko kalubalantar sakamakon da kotun kundin tsarin mulki ta tabbatar ba.

Dan adawar kamaru, Issa Bakary
Dan adawar Kamaru, Bakary yayin yakin neman zabe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ƙara da cewa duk da wasu tashe-tashen hankula da suka faru a yankuna kamar Douala da Garoua, a halin yanzu al’amura sun lafa.

Sakamakon zabe da martanin Bakary

Shugaba Paul Biya, wanda ke mulki tun 1982, ya sake lashe wa’adin mulki na takwas da kaso 53.7 na ƙuri’u, yayin da Tchiroma Bakary ya samu kaso 35.2, bisa ga sakamakon kotun tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Hisbah ta soke shirin auren Mai Wushirya da 'Yar Guda, an ji dalili

Tchiroma, wanda bai amince da sakamakon ba, ya shaida wa Reuters cewa ba zai yarda da “zaben da aka murde” ba, kuma bai jin tsoron kama shi ko tsare shi.

A ranar da aka sanar da sakamakon, ya ce wasu mutane dauke da makamai sun bude wuta kan masu zanga-zanga a kusa da gidansa a Garoua, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane biyu.

Ya ce wannan hari alama ce ta yadda gwamnati ke kokarin murkushe ‘yan adawa ta hanyar amfani da karfin soja.

Hukumomin Kamaru za su yi bincike

A yayin da yake jawabi a Yaoundé, Minista Nji ya tabbatar da cewa za a kaddamar da bincike kan dukkanin abubuwan da suka faru kafin zabe da bayan sanar da sakamako.

Ya ce:

“A yayin wadannan hare-hare, wasu daga cikin masu tada zaune tsaye sun rasa rayukansu,”

Haka kuma, wasu jami’an tsaro sun sami munanan raunuka a yayin kokarin da suke yi na dawo da zaman lafiya.

Bakary ya ce ya ci zaben Kamaru

A wani rahoton, kun ci cewa jagoran 'yan adawa a Kamaru, Tchiroma Bakary ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe zaben kasar.

Kara karanta wannan

Sauya kundin mulki: Majalisa ta fara bitar bukatun kirkirar jihohi 55 a Najeriya

Sai dai jim kadan bayan maganar da ya yi, jam'iyyar shugaba Paul Biya ta karyata ikirarin tana cewa ba haka ba ne.

Bakary ya ce ya gano ya lashe zaben ne bayan tattara kuri'un da jama'ar Kamaru suka kada a zaben sugaban kasa da aka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng